Kotun ICC ta yi watsi da bukatar maida shari′ar Gbagbo Abidjan | Labarai | DW | 27.10.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kotun ICC ta yi watsi da bukatar maida shari'ar Gbagbo Abidjan

Su dai lauyoyin wadanda aka takewa hakki a kasar ta Ivory Coast na ganin mayar da sauraren karar zuwa kasar ko Tanzaniya ba shi da wata ma'ana.

Laurent Gbagbo Anhörung Internationaler Gerichtshof in Den Haag

Laurent Gbagbo

Kotun hukunta manyan laifuka ta kasa da kasa ICC a ranar Litinin ta yi watsi da bukatar lauya da ke kare tsohon shugaban kasar Ivory Coast Laurent Gbagbo ta neman a maida sauraran karar wanda yake karewa zuwa birnin Abidjan, abin da kotun ta ki amincewa bisa dalilan da kotun ta danganta da matsalar tsaro.

Wannan mataki da kotun da ke a birnin Hague ta dauka dai na zuwa ne bayan da a watan da ya gabata lauyan tsohon shugaba Gbagbo ya nemi a mayar da sauraren karar zuwa Kudancin kasar ko kuma a kai ta zuwa birnin Arusha na Tanzaniya.

A ranar 10 ga watan Nuwamba ne dai shugaba Gbagbo tare da jagoran 'yan tawaye da ke tare da shugaba Gbagbo Charles Ble Goude za su bayyana a gaban kotun saboda hannunsu a rikicin da ya biyo bayan zaben shugaban kasa a shekarar 2010 abin da ya yi sanadin rasa rayukan mutane 3000.