Kotun Habasha ta sami Mengistu da laifin kisan kiyashi. | Siyasa | DW | 13.12.2006
 1. Inhalt
 2. Navigation
 3. Weitere Inhalte
 4. Metanavigation
 5. Suche
 6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Kotun Habasha ta sami Mengistu da laifin kisan kiyashi.

Bayan ta shafe shekaru 12 tana shari’a, babban kotun ƙasar Habasha, ta sami tsohon shugaban ƙasar, Mengistu Haile Mariam, da laifin kisan ƙare dangi da kuma wasu ƙararrakin da aka ɗauka game da shi. Masharhanta na ganin cewa, alƙalan kotun za su yanke wa tsohon shugaban hukuncin kisa ne dangane da waɗannan laifuffukan. A halin yanzu dai, Mengistu Haile Mariam na zaman gudun hijira ne a ƙasar Zimbabwe, inda shugaban wannan ƙasa Robert Mugabe, tuni ya ba da sanarwar cewa ba zai miƙa shi ga mahukuntan Habashan ba.

Tsohon shugaban Habasha, Mengistu Haile Mariam.

Tsohon shugaban Habasha, Mengistu Haile Mariam.

A zaman ƙarshe da ta yi, babban kotun ƙasar Habasha, ta sami tsohon shugaban ƙasar, Mengistu Haile Mariam, da laifin kisan kiyashi. A ran 28 ga wannan watan ne kuma, ake sa ran kotun za ta yanke masa hukunci game da waɗannan laifuffukan. Masu sa ido a shari’ar dai sun ce bisa dukkan alamu, hukuncin kisa za a yanke masa, duk da cewa ba ya cikin ƙasar.

Tun 1991 ne dai, bayan an hamɓarad da gwamnatinsa, Mengistu Haile Mariam, ya kaurace zuwa Zimbabwe, inda yake zaman gudun hijira. Shugaba Robert Mugabe na Zimbabwen, ya bayyana cewa, Mengistu, babban baƙon ƙasar ne, kuma zai iya ci gaba da zama nan har tsawon duk lokacin da ya ga dama. Babu shakka, Mugabe na mayar wa Mengistun kyakyawan martani ne, saboda a lokacin yaƙin neman ’yancin Zimbabwen, gwamnatin Habsaha, a ƙarƙashin jagorancin Mengistun, ta taimaka ƙwarai wajen horad da ’yan yaƙin sunƙurun Robert Mugabe.

A halin yanzu dai, rahotanni sun ce Mengistun na zaman jin daɗi ne a Zimbabwen, inda yake facaka da ɗimbin yawan kuɗaɗe da dukiyar da ya tara a lokacin mulkinsa daga 1977 zuwa 1991. Ƙungiyoyin kare hakkin ɗan Adam da jam’iyyun adawa a Zimbabwen sun ce, Mugabe ya naɗa Mengistun a matsayin mai bai wa ƙungiyar leƙen asirin ƙasar shawara.

Shi dai Mengistu, yana cikin ƙananan hafsoshin sojin da suka hamɓarad da gwamnatin sarkin sarakuna Haile Selassie a shekarar 1974. Bayan rigingimun da aka samu a bainar sabuwar gwamnatin mulkin sojin Habashan ne Mengistun ya zamo shugaban ƙasa, inda tare da taimakon tarayyar Sowiet, ya ikafa gwamnatin mulkin gurguzu mai bin aƙidar Marxisanci. A wannan lokacin dai, an yi ta kashe-kashe a ƙasar ta Habasha. A mulkin kama karyar da ya yi, ana zargin Mengistun da halaka ɗaruruwan abokan hamayyarsa, a cikinsu har da janar-janar na soji, da shugabannin coci-coci da ma fararen hula. Hargitsin da ƙasar ta shiga ciki ne ma ya janyo bala’in yunwa da farin nan da Habashan ta yi ta fama da shi a shekarar 1984, waɗanda suka janyo hankullan ƙasashen duniya zuwa ƙasar. Kusan rayuka miliyan ɗaya ne suka salwanta, sakamakon wannan bala’in.

Mengistu dai, ya ci gaba da mulki a Habashan, har zuwa lokacin juyin juya hali a ƙasashen gabashin Turai, abin da ya janyo wargajewar tarayyar Sowiet, da sauran gwamnatocin ƙasashen gabashin Turan masu bin mulkin gurguzu. Kai tsaye ne dai, ya rasa samun taimako daga abokan burminsa, kamarsu tarayyar Sowiet, da Kuba da Jamus ta Gabas. Hakan dai ya gurgunta gwamnatinsa, abin da ya bai wa ’yan tawayen da ke yaƙansa damar shan ƙarfin sojojinsa har ma da kame babban birnin ƙasar, Addis Ababa a cikin watan Mayun 1991. Tun wannan lokacin ne dai Mengistu, ya yi ƙaura da iyalinsa zuwa Zimbabwe.

Daga bisani ne kuma, aka gudanad da zaɓe a ka kafa gwamnatin mulkin dimukraɗiyya karƙashin jagorancin tsohon madugun ’yan tawaye, kuma Firamiya na yanzu, Meles Zenawi. Gwamnatinsa dai ta lashi takobin yi wa tsarin mulkin kwaminisanci da ta gada daga Mengistun ne kwaskwarima.

Amma a halin da ake ciki dai, ɓangarori dama na kare hakkin bil’Adama na zargin sabuwar gwamnatin ma da take hakkokin al’umman ƙasar. Janar Tamene Dilnesahu, tsohon jakadan Habashan a Rasha, a lokacin mulkin Mengistu, wanda a halin yanzu yake zaman gudun hijira a birnin London, ya amince da mulkin kama karya da gwamnatin Mengistun ta yi. Amma kuma, ya ce wannan sabuwar gwamnatin ta Meles Zenawi ma, ba ta da wata hujja ta yi wa Mengistun shari’a, saboda ita ma take hakkin ɗan Adam da yi kuma take ta yi, ya fi na Mengistun ma muni:-

„Al’umman Habashan ne kawai za su iya yanke wa Mengistu hukunci, ba wannan gwamnatin ba. Ta halaka dimbin yawan mutane fiye ma da gwmantain Mengistu. Alƙaln kotun duk ’yan kurar gwamnatin ne. Sabili da haka na ke ganin wannan gwamnatin, ba ta da ikon yanke hukunci kan tsoffin shugabannin da ta gaji mulki daga gare su.“

 • Kwanan wata 13.12.2006
 • Mawallafi YAHAYA AHMED
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink https://p.dw.com/p/Btx5
 • Kwanan wata 13.12.2006
 • Mawallafi YAHAYA AHMED
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink https://p.dw.com/p/Btx5