Kotun Gini ta amince da zaben ′yan majalisu | Labarai | DW | 16.11.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kotun Gini ta amince da zaben 'yan majalisu

Kotun kolin kasar Gini ta yi watsi da karar kalubalantar sakamakon zaben 'yan majalisu

Kotun kolin kasar Gini ta yi watsi da duk kararraki da aka daukaka ana kalubalantar sakamakon zaben 'yan majalisu da aka gudanar a karshen watan Satumba.

Jam'iyya mai mulki ta Shugaba Alpha Conde ta lashe kujeru 53 daga cikin kujeru 114 na majalisar dokokin kasar, inda jam'iyyar ta rasa cikekken rinjayen da take bukata cikin majalisar. 'Yan adawa sun yi zargin tafka magudi.

Zaben 'yan majalisu shi ne matakin karshe bisa shirin mayar da kasar ta Gini Conakry da ke yankin yammacin Afirka bisa turbar demokaradiyya da aka fara tun shekara ta 2008.

Mawallafi: Suleiman Babayo
Edita: Saleh Umar Saleh