Kotun Gambiya ta dage zama kan karar zabe | Labarai | DW | 10.01.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kotun Gambiya ta dage zama kan karar zabe

Shugaban kotun kolin kasar Gambiya ya ce ba a iya zama do sauraran karar da Yahya Jammeh ya shigar kan zaben shugaban kasa ba saboda rashin alkalai.

Bisa dalilai na rashin halatar isassun alkalai, Kotun kolin kasar Gambia ta dage zaman sauraran karar da shugaba Yahya Jammeh ya shigar gabanta don kalubalantar sakamakon zabe. A lokacin da yake bayani a birnin Banjul, shugaban wannan kotu Emmanuel Fagbenle ya ce ya tuntubi alkalai daga kasashe makwabta don su taimaka. Amma ana ji cewar za a shafe watanni kafin kotun ta yanke hukunci kan karar zabne, sakamakon jinkirin isowar alkalai daga Najeriya da Saliyo zuwa Gambiya.

Shi shugaba mai barin gado Yahya Jammeh ya fara amincewa da shan kaye, kafin daga bisani ya nemi kotun koli ta soke sakamakon zaben shugaban kasa saboda kura-kuran da aka fusaknta wajen shirya zabe da kidaya kuri'u. Wasu shugabannin kasashen Afirka ta yamma  a karkashin jagorancin Muhammadu Buhari na Nijeriya za su sake komawa kasar ta Gambiya don neman Yahya Jammeh ya sauka daga mulki cikin girma da arziki.