Kotun EU ta amince da haramcin dankwali | Labarai | DW | 14.03.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kotun EU ta amince da haramcin dankwali

A hukuncin da ta yanke kotun Tarayyar Turai ta ce kamfanoni na da dama bisa wasu sharudda su hana ma'aikatansu musulmi daura dankwali ko sanya wani abu mai alamar addini.

Hukuncin shine irinsa na farko da kotun ta yanke kan wani batu mai zafi na siyasa a fadin tarayyar Turai.

Hukuncin ya danganci wasu kararraki biyu ne da wata 'yar Belgium da kuma wata 'yar Faransa dukkaninsu musulmai suka shigar ne domin kalubalantar sallamar su daga aiki da ma'aikatun da suke yiwa aiki suka yi bisa kin cire dankwali.

Bugu da kari hukuncin ya fayyace tambayar da aka dade ana yi game da kwarya-kwaryar haramcin da wasu kasashe suka yi ko matakin hana amfani da alamomin addini na iya hadawa da wuraren ayyuka.

Kotun ta ce matakin da wani kamfanin Belgium G4S ya dauka na haramtawa ma'aikatansa dake hulda da kwastomomi sanya wani abu da zai baiyana a zahiri wanda ya danganci addini ko alama ta siyasa ba wariya bace ko nuna banbanci ga ma'aikaciyar dake aikin karbar baki a wani kamfanin manhaja sadarwa dake Belgium Samira Achibita da kamfanin ya sallama a shekarar 2006 bisa daura dankwali yayin da take bakin aiki.

Tuni kungiyoyin kare hakkin bil Adama suka fara maida martani da cewa hukuncin zai jawo sallamar mata musulmi da yawa daga wuraren ayyuka.