Kotun ECOWAS ta yi watsi da kundin zaben Burkina Faso | Labarai | DW | 13.07.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kotun ECOWAS ta yi watsi da kundin zaben Burkina Faso

Kotun ECOWAS mai cibiya a birnin Abuja na Najeriya, ta yi watsi da batun haramta wa wasu 'yan kasar Burkina Faso tsayawa takara a zaben shugaban kasar mai zuwa.

Kotun ECOWAS ko CEDEAO ta kasashen yammacin Afirka ta yi watsi da kundin zaben kasar Burkina Faso wanda ya haramta wa na kusa da tsohon shugaban kasar Blaise Compaore shiga takara a zaben shugaban kasar da zai gudana a watan Octoba mai zuwa. A watan Afrilu ne dai majalisar dokokin kasar ta rikon kwarya ta amince da wannan kundi da ya haramtawa duk wani wanda ya baiwa tsohon shugaban kasar goyon baya wajan canza kundin tsarin mulkin kasar tsayawa takara.

Kotun ta CEDEAO ta ce canza kundin zaben kasar ta Burkina Faso da majalisar rikon kwaryar kasar ta yi, take inci ne na tsayawa takara ga wasu 'yan kasar ta Burkina Faso, inda kotun ta bada umarnin cire wannan sashe domin baiwa duk 'yan kasar damar tsayawa takara.

A kalla dai jam'iyyun siyasar kasar ta Burkina Faso guda bakoye ne cikinsu har da jam'iyyar CDP ta tsofon shugaban kasar Blaise Compaore su ka shigar da karan kundin zaben a watan Yuni da ya gabata a gaban kotun da ECOWAS, kuma ganin cewa kasar ta Burkina Faso na a matsayin memba, dole ne ta yi aiki da wannan hukunci.