Kotun ECOWAS ta ci Najeriya Tarar Euro dubu 50 | Labarai | DW | 11.06.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kotun ECOWAS ta ci Najeriya Tarar Euro dubu 50

Samakamon wani kara da aka shigar a gabanta, kan yadda sojojin Najeriya suka ci zarafin wasu mutane, kotun ta samu Najeriya da laifi.

Najeriya dai an sameta da laifi ne kan batun korar wasu mutane 'yan zauna gari banza, da sojoji suka wulakanta a ranar 12 ga watan Octoba na 2009 a yankin Neja Delta, korar da ta haddasa mutuwar mutun guda, tare da jikkata wasu mutanen a kalla 12.

Kotun ta ECOWAS dai tace sojojin da suka kori mutanen, basu da wata hujja ta buda musu wuta, dan haka kasar Najeriya zata biya diya da Euro dubu 50, kwatankwacin naira milian 11.

Kotun ta kara da cewa gwamnatin ta Nageriya ta nuna gazawa, wajan bada kariya, da kuma mutunta hakkokin mutanen dake zaune cikin lumana.

Tuni dai Darektan kungiyar Amnesty International bangaren Afirka, ya yaba wannan hukunci, tare da jinjinawa al'ummar yanki da tabi kadun hakkokin ta, kuma hakan yana nunar da cewa gwamnatoci baza su ci gaba da cin zarafin al'ummomin su, ba tare da fuskantar wani hukunci ba.

Mawallafi: Salissou Boukari
Edita : Usman Shehu Usman