Kotun duniya ta daure Bemba | Siyasa | DW | 21.06.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Kotun duniya ta daure Bemba

Kotun duniya ta daure Jean-Pierre Bemba tsohon mataimakin shugaban Jamhuriyar Demokaradiyyar Kwango da aka samu da laifukan yaki.

Kotun duniya da ke hukunta masu laifukan yaki da ke birnin Hague na kasar Holland ta yanke hukuncin daurin shekaru 18 ga Jean-Pierre Bemba tsohon mataimakin shugaban kasar Jamhuriyar Demokaradiyyar Kwango, bisa laifukan da dakarunsa na sa-kai suka aiwatar a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya.

Bemba dan shekaru 53 da haihuwa tun cikin watan Maris kotun ta same shi da laifi kan lamarin ta'asa na shekara ta 2002 zuwa 2003 a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya da suka hada da fyade kuma ya kasance na farko da kotun ta samu da laifi bisa aikin da dakarun da ke karkashin ikonsa suka aikata. Ita dai kotun ta duniya ta kama Bemba da laifui saboda yadda ya gaza tsawatar wa dakarun da ke karkashin ikonsa.