Kotun Afirka ta Kudu ta jefa makomar shugaban kasar cikin kasada | Labarai | DW | 29.12.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kotun Afirka ta Kudu ta jefa makomar shugaban kasar cikin kasada

Kotun ta yanke hukuncin da zai iya janyo tsige Shugaba Jacob Zuma na Afirka ta Kudu daga kan madafun iko bisa amfani da kudaden gyara gida ta hanyar da ta saba doka.

Kotun tsarin mulkin kasar Afirka ta Kudu ta zartas da hukuncin cewa majalisar dokokin kasar ta gaza wajen rashin ladaftar da Shugaba Jacob Zuma game da amfani da kudade domin kyara gidansa ta hanyar da ta saba ka'ida lamarin da zai iya janyo jefa kuri'ar tsige shugaban.

'Yan adawa suka shigar da kara bisa zargin kakakin majalisar dokoki da rashin bin hanyoyin da suka dace na hukunta Shugaba Zuma saboda rashin bin matakan da hukumar yaki da cin hanci da rasha ta shinfida. Akwai yuwuwar Shugaba Jacob Zuma zai shiga tsaka mai wuya, sakamakaon yadda mataimakinsa Cyril Ramaphosa ya karbi ragamar tafiyar da jam'iyyar ANC mai mulkin Afirka ta Kudu, bayan samun nasara kan tsohuwar matar Zuma, wato Nkosazana Dlamini-Zuma.