Kotu ta yankewa Hama Amadou hukuncin zaman sarka | BATUTUWA | DW | 13.03.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

BATUTUWA

Kotu ta yankewa Hama Amadou hukuncin zaman sarka

Kotun daukaka kara a Jamhuriyar Nijar ta yankewa tsohon Shugaban majalisar dokoki Hama Amadou hukunci daurin shekara guda.

Tsohon Shugaban majalisar dokoki Hama Amadou

Tsohon Shugaban majalisar dokoki Hama Amadou

A wannan Litinin ne kotun daukaka kara a birnin Yamai na Jamhuriyar Nijar za ta fara sauraran karan tsohon Shugaban majalisar dokokin kana tsohon firaminista kasar Hama Amadou, game da zargin da ake yi masa na samunsa da hannu a cikin safarar jarirai.Tun farko an shirya shari'ar ce ranar 13 ga watan Faibrairu, amma lauyoyin da ke kare Haman suka bukaci da a dage shari'ar saboda wasu dalilai na tsarin takardu da alkalin alkalai bai bayyana ba, bayan kotun farko ta Majestry ta ce ba da hurumin yin shari'ar. 

Soma yin shari'ar zai kasance cikin wani hali na dagulewar al'amura a Nijar, inda kotun za ta saurari mutane kusan talatin wadanda suka hada da wani tsohon minista  da ma'aikatan bankin da  wasu sojoji, sannan da mai dakin tsohon Shugaban majalisar dokokin da ma shi kansa da ake zargi da hannu a cinikin Jariran. Jariran da aka sayo daga Najeriya domin 'yantar da su a matsayin 'ya'ya kamar yadda gwamnatin kasar ke zargi. Lamarin na zargin tsohon Shugaban majalisar dokokin Hama Amadou, ya fara ne a cikin watan Yuni na shekara ta 2014 a lokacin Haman na rike da matsayin kakakin majalisar dokoki, kafin daga bisani a kada kuri'ar tsige shi daga matsayin, bayan jam'iyyarsa ta fice daga mulki. Daga nan kuma Hama ya fice daga Nijar zuwa kasar Faransa domin neman mafaka.

Ya dawo Nijar a cikin watan Nuwamba na shekara ta 2015, daf da lokacin da ake shirin gudanar da zaben shugaban kasa zagaye na biyu, take yanke kuma aka kama shi aka kuma garkameshi a gidan kurkuku sai dai an bashi izinin ya yi kampe a zaben kasar da ya gabata tun daga gidan kason da ake tsare da shi, sai dai kuma bai yi ba. Gabannin yin zagaye na biyu na zaben a sake tafiya da Haman cikin gaggawa zuwa Faransa saboda rashin lafiyar da yake fama da ita wanda tun daga wanan lokaci bai sake komawa Nijar ba.

Hama Amadoun dai da mai dakinsa, na musunta zargin sayen jariran suna masu cewar kazafi ne na siyasa domin taka masa birki. A yayin da dukkanin sauran mutane 30 da aka kama a cikin harkar jariran su aka sallamesu daga gidan kaso. Klaas Van Waraven wani masanin kimiyar siyasa ne da kuma tarihi wanda ya gudanar da nazarce-nazarce da dama a kasashen Afrika ciki har da Nijar wanda kuma malami a jami'ar Leiden. Ya ce  ko da gwamnati na zargin wani da aikata wani laifi ta gabatar da shi a gaban kuliya, alal hakika kotu ce ke da cikakken 'yanci, gwamnati ba ta da sukuni ko izini na bayar da umarni ga kotun da ta yi abin da take so.

Babu shakka nasara da Mahamadou Issoufou ya samu da gaggarumin rinjaye a zagaye na biyu na zaben  ta bashi damar murkushe 'yan adawa a Nijar, wanda manazarta ke yi masa kallon yadda yake kalawa inda ba gaba da shi da 'yan jamiyyarsa ta PNDS Tarraya, to amma wannan sharia da za a soma a wannan Litinin, daya daga cikin lauyoyin dake kare tsohon kakakin majalisar dokoki Maitre Boubakar Mossi wanda ya ce a baya an yi wa Hama Amadoun rashin adalci a yanzu ya ce suna jiran kotun ta tabbatar da gaskiya.

Idan har kotu ta tabbatar tana da cikakken 'yanci, bani da fargaba cewar wadanda nake karewa, za a wanke su daga duk wani zargin da ake yi musu, amma magana ta karshe tana cikin hannun alkalai na tabbatar da cewar suna da cikakken yanci

 

Sauti da bidiyo akan labarin