Kotu ta yanke wa Simone Gbagbo hukuncin ɗaurin shekaru 20 | Labarai | DW | 10.03.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kotu ta yanke wa Simone Gbagbo hukuncin ɗaurin shekaru 20

An ɗaure matar tsohon shugaban ƙasar Cote d'Ivoire kan laifukan da aka aiwatar bayan zaɓe.

Wata kotun ƙasar Cote d'Ivoire ta ɗaure Simone Gbagbo, matar tsohon Shugaba Laurent Gbagbo na tsawon shekaru 20. An sameta da laifin zagon ƙasa wa tsaron ƙasa bayan zaɓen shugaban ƙasa na shekara ta 2010, abin da ya janyo tashin hankali a ƙarshen shekara ta 2010 zuwa 2011 da ya yi sanadiyyar hallaka mutane 3,000.

An zargi Simone Gbagbo 'yar shekaru 65, da goyon bayan mijinta Laurent Gbagbo wanda ya ƙi amincewa da shan kayi a zaɓen watan Nowamba na shekara ta 2010, wanda hukumar zaɓe ta tabbtar cewa Alassane Ouattara ya lashe.

Yanzu haka mijinta tsohon Shugaba Gbagbo yana fuskanatar tuhuma kan wannan tashin hankali a kotun duniya da ke hukunta masu manyan laifukan yaƙi.