Kotu ta yanke hukunci kan tsoffin ′yan Khmer Rouge | Labarai | DW | 07.08.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kotu ta yanke hukunci kan tsoffin 'yan Khmer Rouge

Mutane biyun da suka yi saura a tsohuwar gwamnatin Kambodiyar da ake zargi da azabtar da fararen hula, an yanke mu su hukuncin daurin rai da rai.

Wata kotu a birnin Phnom Penh na kasar Kambodiya da ke samun goyon bayan Majalisar Dinkin Duniya, ta zartar da hukucin daurin rai da rai ga wasu tsofin jami'an gwamnatin Khmer Rouge guda biyu wadanda ta samu da laifin aikata kisan gilla da azabtar da fararen hula. Mutanen, Nuon Chea mai shekaru 88 da Kieu Shapan mai shekaru 83 wanda shine tsohon shugaban kasar ta Kambodiya a tsohuwar gwamnatin kama karya ta Kampuchiya, na da hannu wajen aiwatar da kisan mutane miliyan biyu a Kambodiya tsakanin shekara ta 1975 zuwa shekara ta 1979. Wannan shi ne hukunci na farko da wata kotun ta yanke a kan tsaffin jami'an tsohuwar gwamnatin ta Khmer Rouge, wadanda suke a raye.

Mawallafi: Abdourrahamane Hassane
Edita: Umaru Aliyu