Kotu ta wanke Abdurasheed Maina kan fensho | Siyasa | DW | 05.08.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Kotu ta wanke Abdurasheed Maina kan fensho

Ci gaba da muhawara bayan da kotu a Najeriya ta bada umurnin a maida shugaban kwamitin binciken kudin fensho, Abdurasheed Maina kan mukaminsa, duk da zargin cin rashawa.

Umurnin da kotun kula da hakokin ma'aikata ta bayar na a mayar da shugaban kwamitin da shugaban Najeriya ya kafa a game da kudadden fansho a kan aikinsa Abdurasheeed Maina duk da cewa ana zarginsa da karkatar da kudadden yan fansho da suka kai Naira bilyan 180 ya haifar da takaddama da ma maida murtanai a kan batun.

To an dai kaiga shiga yar boyo a tsakanin majalisar datawan Najeriyar da Alhaji Abdurasheed Maina, wanda ya jagoranci kwamitin da shugaban Najeriya ya kafa daya binciko sama da fadin da aka dade ana tafkawa a fannin kudadden fanshon Najeriyar saboda fuskantar zargin day an majalisar suka yi mashi na cewa shi kansa da aka sa ya bincika al'amarin ya kaiga karkatar da kudadden yan fanshon da suka kai Naira milyan dubu 180.

Nigeria Korruption

Yaki da cin rashawa a Najeriya

To sai dai bayan boyo na tsawon lokaci daya yi da ma sanar da dakatar dashi daga aiki da shugaban ma'aikatan Najeriya ya yi, sai gashi wata kotu a Abuja ta wanke shi daga aikata duk wani laifi, tare da bada umurnin a mayar dashi kan aikinsa. Wannan lamari da tuni ya harzuka tsofafin ma'aikana gwamnatin Najeriyar da ya kaiga wasunsu mutuwa suna jiran layin karabar kudadensu na fansho. Alahaji Ali Abacha shine shugaban kungiyar yaki da cin hanci da tabbatar da adalci a Najeriyar da ke adawa da wanana mataki.

‘'Wanan abu da kotu ta yi ina ganin ta yi shine bisa kan rashin isa don kotu itace karshen matakin wanda abu ya dame shi zai kai kara, amma yau a ce an san wanan mutum ya yi laifi, ya yi ta'asa, ya jefa mutane cikin wahala sun jikkata, amma ace kotu ta wanke shi. Don haka muna kira ga babbar jojin Najeriya da ya duba wanan shari'a, don haka dan Adam ina zashi kenan?''

Majalisar datawan Najeriyar da ta kasancxe mai ja-in-ja da shugaban kwamitin da ya kasance a tsakiyar wannan al'mari, wacce duk gayyatar da ta yi mashi na ya bayyana a gareta ta faskara, hatta sammacin kama shi da sifeto janar na ‘yan sandan Najeriya ya bayar ya zama zancen iska, abinda ya kara karfafa zargin cewa fadar shugaban Najeriya na bashi kariya duk da musanta hakan da ta yi. Sanata Kabiru Ibrahin Gaya shine mataimakin shugaban kwamitin majalisar da suka binciko zargin wannan badakalla yace wanan mumunan koma baya ne ga batun cin hanci da rashawa a Najeriya.

‘'Mun yi iya kokarinmu tsakaninmu da Allah a kan wanan tsari kuma naji dadi an nunawa yan Najeriya kai tsaye an ji irin tambayoyin da muka yi, mun yi Karin ganin an yi gaskiya, amma ba' son a yi gaskiyar. Wanan abu da ban mamaki da ban tsoro a Najeriya kuma wanan ya dada baiwa cin hanci da rashawa gindin zama''.

Wahlen Nigeria Präsident Goodluck Jonathan Stimmabgabe

Shugaban kasa Goodluck Jonathan da uwargidansa

Shi dai shugaban kwamitin da ya binciko makudan kudadden yan fanshon da aka sace da yace sun kai Naira bilyan 251 Abdursheeed Maina ya dage kan cewa shi kam bai aikata laifin ake zarginsa ba. A wata hira da na yi da shi na tambaye shi ko zai yarda ya fuskanci bincike a kan wanan zargi?

‘'Kwarai da gaske wallahi in aka bani dama ko da yaushe ko an kirani sau dubu ne zan je, duk sanda aka kirani ko sau dubu ne zan je''.

Afkawa kudadden fansho da wasu jami'an gwamnati da suka makance da matsalar cin hanci da rashawa a Najeriya na nuna kara kazancewar da matsalar ke yi, domin bias al'ada kudadden yan fansho abin kulawa ne ga kowane ma'aikaci zai yi ritaya das a ran cin moriyar lamarin.

Zargin aiwatar da sharioin da sukan sabawa hankali a batun cin hanci da rashawa dai ya kaiga sanya majalisar kula da harkokin shari'a ladabtara da wasu alkalai a kan wuce iyaka, abinda ke kara jefa tababa a kan gaskiyar ikirarain da gwamnati ke yin a yaki da cin hanci da rashawa a kasar.

Mawallafi: Uwais Abubakar Idris
Edita: Umaru Aliyu