1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kotu ta hana gwamnati killace Sarki Sunusi

Uwais Abubakar Idris ZU
March 13, 2020

Babbar Kotu da ke Abuja ta bada umarni hukumomin tsaron Najeriya su saki tsohon Sarkin Kano Muhammadu Sanusi daga wani gari a jihar Nassarawa inda ake tsare da shi bayan cire shi daga sarautar Kano.

https://p.dw.com/p/3ZO0c
Nigeria neuer Emir von Kano Sanusi Lamido Sanusi
Hoto: Amino Abubakar/AFP/Getty Images

Lauyoyin tsohon sarkin ne suka shigar da kara a gaban kotun Abuja babban birnin tarayyar kasar. Tun a safiyar wannan Juma’ar lauyoyi da magoya bayan tsohon sarkin Kano suka hallara a gaban kotun ta Abuja don ganin yadda za ta kaya.

Tawagar lauyoyin da ke kare tsohon sarkin sun bukaci kotu ta tabbatar wa wanda suke karewa  ‘yancinsa na walwala domin a fahimtarsu ci gaba da tsare shi da sufeto janar na ‘yan sanda da shugaban hukumar tsaro ta farin kaya ke yi ya sabawa wannan yanci na tsohon sarkin.

A hukuncin da ya yanke mai shari’a Anwuli Chikere ya bada umurnin a mika wannan hukunci ga mutanen da aka yi kara domin su hanzarta sakin sarkin.

 ‘’Kotu ta bada umarnin lallai a sake shi tun da babu wani dalili a hukumance na tsare shi. A don haka muna kokarin yadda za a kai wa babban sufeton 'yan sanda da sauran jami’an tsaro wadanda muka yi kara don su aiwatar da wannan umarni na kotu’’ inji Barista Abubakar Balarabe  Mahmoud daya daga cikin lauyoyin tsohon Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II.

Sanusi Lamido Sanusi Gouverneur Zentralbank Nigeria
A ranar Litinin 09.03.2020 gwamnatin jihar Kano ta sanar da cire Tsohon Sarkin Kano Muhammadu Sunusi IIHoto: Aminu Abubakar/AFP/Getty Images

Lauyoyin gwamnmati da ke wajen shari’ar dai sun ki cewa ‘uffan’ a kan sakamakon shari’ar da ya umarci su yi ladabi ga hukuncin da kotun ta zartas. To sai dai wasu 'yan Najeriya na ganin gaba-daya rikicin da ya faru a tsakanin tsohon sarkin da gwamnatin jihar Kano ya nuna cewa ba a yi amfani da dattaku ba.

’’Wannan lamarin ya tona asirin mutanen arewacin Najeriya, na farko ya nuna cewa mu mutane ne wadanda ba ma iya yafe wa juna, na biyu ya nuna cewa mu mutane ne wadanda ba mu da hakuri, sannan ya nuna cewa ba wai halin da kasar ke ciki ya dame mu ba. Idan an yi mana abu sai mun ga karshen mutum’’ inji tsohon ministan wasannin Najeriya Solomon Dalung.

Duk da cewa dai kotun ta umarci a bar tsohon sarkin ya tafi duk inda yake son zuwa a Najeriya, amma rahotanni sun ce kawo lokacin rubuta wannan labari an hana shi ziyartar jihar Kano inda ya yi sarauta.

Nigeria Sanusi Lamido Sanusi
Kafin Sarki Sunusi ya samu mukamin Sarkin Kano a shekara ta 2014 ya jagoranci Babban Bankin Najeriya na wasu shekaru.Hoto: Amino Abubakar/AFP/Getty Images

Rahotannin da ke fito kuwa daga jihar Nasarawa sun ce a ranar Juma’ar nan tsohon sarkin ne ya jagoranci sallar juma’a a garin Awe, inda ake tsare da shi.

Sallar juma’a dai ibada ce da musulmi ke yi a cikin jam’i a kowane mako. A lokacin da yake kan gadon sarauta a birnin Kano tsohon sarkin ya rinka jagorantar irin wannan ibada.

A shekara ta 2014 ne dai aka nada tsohon Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II a matsayin Sarkin Kano, masarautar da ke da matukar daraja a arewacin Najeriya. Kafin a nada shi sarkin Kano, ya jagoranci babban bankin Najeriya na wasu shekaru. Sai dai kuma a ranar Litinin 09.03.2020 gwamnatin jihar Kano ta sanar da tube masa rawani daga mukamin sarkin Kano. Daga nan gwamnatin ta dauke shi ta kai shi wani kauye a jihar Nasarawa da ke tsakiyar Najeriya don yin biyayya ga wata tsohuwar al'ada a kasar Hausa, wace ta tanadi yi wa sarkin da aka sauke hijira zuwa wani gari na dabam ba tare da amincewarsa ba. Kungiyoyi ciki har da Amnesty International sun ce keta 'yancin dan adam ne. Yanzu jama'a sun zura ido su gani ko gwamnatin Najeriya za ta yi biyayya ga umarnin kotu na ranar Juma'a.