SiyasaLatin Amurka
Kotun kolin Venezuela ta tabbatar da zaben kasar
August 22, 2024Talla
A wannan Kotun kolin kasar Venezuela ta tabbatar da nasarar da Shugaba Nicolas Maduro ya samu a zaben da ya gudana ranar 28 ga watan jiya na Yuli, tare da kayar da jagoran 'yan adawa Edmundo Gonzalez, abin da ya tabbatar da ikirarin jam'iyya mai mulki na lashe zaben da 'yan adawa suke zargin tafka kazamin magudi.
Tun bayan bayyana sakamakon zaben ake samun zanga-zangar nuna adawa da sake ayyana Shugaba Maduro a matsayin wanda ya sake samun sabon wa'adin mulki a kasar ta Venezuela da ke yankin Latin Amurka.