Kotu ta saki wasu na kusa da Riek Machar | Labarai | DW | 25.04.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kotu ta saki wasu na kusa da Riek Machar

Ana sa ran samun sasauci a rikicin kasar Sudan ta Kudu bayan da kotu ta saki mutanen da ake zagi da laifin juyin mulki.

Wata kotu a Juba babban birnin kasar Sudan ta Kudu ta salami wasu mutane guda hudu, na kusa da madugun yan tawayen kasar Riek Machar da akayi zargi da laifin yunkurin juyin mulki.

A jiya Alhamis ne dai, Ministan Shari'ar kasar Paulino Wanawilla, ya shigar da takardar neman duba wannan shari'a tare da neman kawo karshen ta a wani matani na neman zuba ruwa a wutar rikicin dake ci gaba da ruruwa a wannan jaririyar kasa.

Jim kadan dai, bayan fitowar su daga kotun, magoya bayan su suka barke da sowa da tabi, dan nuna farin cikin su da ganin wadannan jagorori na su.

Mutanen hudu da suka hada da Wani Janar na Soja, da tsofon Ministan tsaron kasar, da tsofon Jakadan kasar ta a Amirka, da kuma tsofon Maitamakin Ministan tsaron kasar, an kama su ne tun a tsakiyar watan Disamba daya gabata, wanda kuma shine ya kara ririta rikicin kasar ta Sudan ta Kudu da a halin yanzu yayi sanadiyar rasuwas mutane da dama.

Mawallafi: Salissou Boukari
Edita : Pinado Abdu Waba