Kotu ta haramta tura sojoji wurin zaɓe | Siyasa | DW | 24.03.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Kotu ta haramta tura sojoji wurin zaɓe

A Najeriya wani abin da ke zaman alamun sauyi ga batun tsoma bakin soja cikin harkokin zaɓe, wata kotu a Lagos ta jaddada haramci ga shugaban ƙasar na tura sojoji a runfuna zaɓe.

Kama daga jihar Ekiti in da har yanzu ake kallon rawar ta soja wajen tabbatar da nasarar jam'iyyar PDP ya zuwa rawarsu a zauren majalisar wakilan Najeriya, sannan daga baya tsohon tarihin da ke cike da miki a cikin sa dai an daɗe ana zargin jami'an tsaron Tarayyar Najeriya da fitsare kafarsu da nufin goyon baya ga yan siyasar mulki a cikin ƙasar. Sojan ƙasar ta Najeriya ne dai ga misali suka nemi dage zaɓuɓɓukan ƙasar bisa hujja ta tsaro dama rashin shiri da adawar ƙasar ta fassara da ƙoƙari na ceto ga shugaban ƙasar da ke shirin shan kaye can baya.

To sai dai kuma wani hukuncin wata kotun Tarayya a cikin birnin Lagos dai, na shirin sauya tunanin sojan ƙasar da a baya aka sha nunawa a gaban alƙalai da zummar tabbatar da magudin zaɓe a ɓangare na adawa.Hukuncin da ke zaman irin sa na biyu cikin tsawon wata guda dai, ya haramta wa shugaban ƙasar janyo soja zuwa ga rumfunan zaɓe 120,000 da ƙasar ke da su a ranar zaɓen, ko dai don ba da tsaro ko kuma da nufin taimaka wa ko wacce jam'iyya samun nasara.Sabon hukuncin kuma da ke kama da babbar salla ga masu adawar, da ke tunanin sun ji jiki can baya a hannun sojan da ya kare da taimaka wa jam'iyyar PDP, maimakon tabbatar da tsaro ga masu zaƁe. A fadar Injiniya Buba Galadima da ke zaman jigon a APC da kuma ya jagoranci adawa da isar soja ga rumfar zaƁe.

"Waɗanda suke tura sojojin nan abokan adawarmu ne, in sun je, su za su yi wa aiki su tursasa wa talakawa da ba su san hakkinsu ba. Wani lokaci ma da su ake kwatar akwatunan zaɓe. In ma baiwa gwamnatin Najeriya shawara ina bai wa shugabannin sojan shawara, su sani cewar su sojan ƙasa ne, bana wani mutum ba, don yana riƙe da mulki a yau. Saboda duk abin da ya biyo baya shugabansu na iya fuskantar kotun duniya”

Shawara ga shanun gwamna, ko kuma ƙoƙari na jari hujja dai, ko bayan masu takama da adawar dai a can cikin gidan PDP ma ra'ayi ya karye a tsakanin masu tunanin, sai soja ko kafar katako, da kuma masu ganin an saba bisa tsari dama ƙoƙari na nuna ta kusa rushewa cikin ƙasar a tunanin Dr Umar Ardo da ke zaman dan PDP kuma masani a harkar sojan.“ Inda ka ga ana kawo soja cikin zabe, to kasashe da ke da alamun rushewa. Don me za mu sa kanmu a haka. Da ana kawo sojojin ne ai ba a kawo soja a zaɓuɓɓuka, yan sanda ne aka kawo”

Tana shirin rushewa ko yin kyau dai, ya zuwa yanzu soja na aikin tabbatar da tsaron cikin gida a aƙalla jihohin ƙasar 34 da suka hada da daukacin yankin arewa maso-gabas, da ke fuskantar tawaye, abun da kuma a fadar Bello Sabo Abdulkadir da ke zaman sakataren kungiyar dattawan yankin na Arewa Maso-gabas, ya sanya kyale soja wajibi da nufin karfafa gwiwar zaɓen, ga miliyoyin 'yan zaben da ke da tsoro yanzu.

“Tabbas ganin soja a wuraren da za'yi zaɓe a Arewa Maso-gabas, inda za'a yi zaɓe zai iya kara musu kwarin gwiwa, dama sanin suna da kariya koma me zai faru”

Abin jira a gani dai na zaman tasiri na hukuncin kotunan ƙasar, bisa rawar sojojin da tuni suka nuna alamu na karkata a zaɓɓuɓukan da ke tafe.

Sauti da bidiyo akan labarin