Kotu ta fara sauraron Muhammad Mursi | Labarai | DW | 14.07.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kotu ta fara sauraron Muhammad Mursi

Ana binciken hamɓararren shugaban da shi da wasu manbobin jam'iyyarsa dangane da zargin da ake yi masu na tserewa daga wani gidan kurku na Wadi Natrun.

Ana tsare da mutanen ne a lokacin da aka yi juyin juya halin da ya yi sanadiyyar faɗuwar gwamnatin tsohon shugaban ƙasar Hosny Mubarak,kafin daga bisani a gano cewar sun arce daga gidan tsaron.

Masu yin binciken na buƙatar samun bayyanai kan cewar ko tsohon shugaban da 'yan ƙungiyarsa sun sami tallafin ƙungiyar Hezbullah ta Lebanan ko Hamas ta Falasɗinu a lokacin da lamarin ya faru. Kuma a cikin watan Yuni da ya gabata wata kotun ta ce ƙungiyoyin na Hamas da Hezbullah suna da hannu waja a cikin lamarin.

Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Zainab Mohammed Abubakar