Kotu ta daure wasu ′yan Najeriya a Faransa | Labarai | DW | 04.06.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kotu ta daure wasu 'yan Najeriya a Faransa

Wata kotun birnin Marseille na kasar Faransa ta yankewa wasu mutane guda hudu 'yan Najeriya hukuncin dauri bisa kamasu da laifin safarar 'yan mata Domin karuwanci.

Afrika Nigeria Prostitution

A kalla mutane hudu da suka hada da mata biyu da maza biyu aka kama da laifin kawo 'yan mata kimanin 20 daga Najeriya ya zuwa birnin na Marseille kuma suka saka su a harkar karuwanci ta hanyar tilasta musu ko kuma yi musu asiri.

Matan biyu dai da ke jagorancin wannan kungiya, da suka hada da Angela Asemota da ake kira da sunan MamaTwins, da kuma Grace Jecope da ake kira Franca, an yanke musu hukuncin daurin shekaru hudu-hudu gami da tarar Euro dubu 15. Da farko dai babban alkalin kotun ya nemi da a yanke musu hukunci dauri na shekaru goma-goma a gidan kaso da kuma tara ta Euro dubu 550.