Kotu ta daure Karadzic na tsawon shekara 40 | Labarai | DW | 24.03.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kotu ta daure Karadzic na tsawon shekara 40

Kotun da ke hukunta manyan laifukan yaki ta yanke wa tsohon shugaban Sabiyawan Bosniya Radovan Karadzic hukunci mai tsauri bisa laifin aikata kisan kiyashi.

Kotun kasa da kasa ta sameshi da hannu a kashe-kashe da aka aikata a Srebrenica shekaru 21 da suka gabata, lamarin da ya sa ta yanke wa tsohon shugaban Sabiyawan Bosniya Radovan karadjic hukunci daurin shekaru 40 a gidan yari. Tuni lawyoyinsa suka ce za su daukaka kara bayan da aka sami Karadzic da laifuka 11 daga cikin 12 da ake zarginsa da aikatawa.

Karkashin jagorancin Radovan Karadzic ne sojojin Sabiya suka yi wa yankin Srebrenica da ke karkashin kulawar Majalisar Dinkin Duniya tsinke a shekarar 1995, inda suka halaka Musulmi maza 8000.

Wadannan kashe-kashen su ne ta'asa mafi muni da aka aikata a wata kasa ta Turai tun bayan kammala yakin duniya na biyu. A jimlance dai mutane dubu 100 ne suka rasa rayukansu a yakin da aka yi fama da shi a Bosniya tsakanin shekarar 1992 da 1995.