Kotu ta daure Hoeneß na Bayern Munich | Labarai | DW | 13.03.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kotu ta daure Hoeneß na Bayern Munich

Shekaru uku da watannin shida shugaban Bayern Munich Uli Hoeneß zai yi a gidan yari bayan da kotu ta sameshi da laifin kin biyan haraji na miliyoyin Euro.

Kotun birnin Munich na Jamus ta yanke wa shugaban kungiyar Bayern Munich Uli Hoeneß hukuncin daurin shekaru uku da rabi a gidan yari bayan da ta sameshi da laifin kin biyan haraji. Da farko dai babban alkali da ke shigar da kara ya bukaci a yanke wa Uli Hoeneß hukunci shekaru biyar da rabi a gidan yari. Sai dai lauyan da ke kareshi ya nemi kotu da ta yi wa shugaban Bayern Munich sassauci saboda shi ne ya fallasa kansa da kansa.

UIi Hoeneß Ya yarda cewa ya kamata ya biya hukumomin harajin Jamus miliyoyin Euro bayan wata hada-hadar hannayen jarin da yayi a karkashin wani banki na kasar Switzerland ko kuma Suisse. Ko da shi ke dai wadanda suke da hannayen jari a kungiyar Bayern Munich da ke kudancin Jamus na ci-gaba da goyon bayan Hoeneß, amma kuma ana ganin cewa magoya bayan wannan kungiya za su bukaceshi da ya ajiye aikinsa.

Tuni dai lawyan Uli Hoeneß ya bayyana cewa za su daukaka kara a kotun koli da ke birnin Karlsruhe. Ita dai kungiyar Mayern Munich da Uli Hoeneß ke shugabanta ne ke rike da kofin zakaru na nahiyar Turai a halin yanzu.

Mawallafi: Mouhamadou Awal Balarabe
Edita: Pinado Abdu-Waba