Kotu ta bada umarni kada kuri′a kan Zuma | Labarai | DW | 22.06.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kotu ta bada umarni kada kuri'a kan Zuma

Majalisar dokokin Afirka ta kudu ta sami amincewar kotu na kada kuri'a ko za su tsige shugaban kasar Jacob Zuma ko kuma a'a.

Kotun kolin Afrika ta Kudu ta amince da bai wa 'yan majalisar kasar damar kada kuri'ar sirri don ko a tsige shugaba Jacob Zuma daga mukaminsa ko kuma a'a.

 Sai dai kotun ba ta tsayar da ranar gudanar da zaben ba. Babban alkalin kotun dai ya ce kundin tsarin mulkin kasar ya bai wa kakakin majalisar damar shirya zaben. 

Shugaba Jacob Zuma dai yana fuskantar matsain lamba kan zargin cin hanci da rashawa da kuma matakinsa na yi wa Majalisar kasar garanbawul, Zuma na kara rasa magoya baya har daga jam'yyarsa ta ANC da kuma na adawa da ke kira na ya sauka daga mulkin kasar.