1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kotu a Hague ta janye kara kan Omar Al Bashir

December 16, 2014

A wani mataki da ya zama mummunan koma baya, kotun kasa da kasa a Hague ta janye tuhumar dake kan shugaban Sudan Omar Hassan Al Bashir bisa laifukan kisan kare dangi a Darfur

https://p.dw.com/p/1E5d0
Sudan Präsident Omar al-Bashir 06/2014
Hoto: AFP/Getty Images

Kotun kasa da kasa ta majalisar dinkin duniya mai shari'ar wadanda ake tuhumarsu da aikata manyan laifukan yaki mai mazuninta a birnin The Hague ta sanar da cewar ta dakatar da farautar shugaban kasar Sudan, Omar Hasan Al Bashir da neman gurfanar dashi gabanta, saboda zargin aikata laifukan yaki da kisan kare-dangi a yankin Darfur. Wannan mataki dai mummunan koma baya ne ga kotun, wadda majalisar dinkin duniya ta kafa, domin shari'ar shugabanni masu mulkin kama karya da gallazawa al'ummar su.

Kawo karshen binciken da kotun ta kasa da kasa take yi a game da laifukan kisan kare dangi a Darfur, ya tabbatar da karshen duk fatan da ake da ita, game da yiwuwar samun zaman lafiya da tabbatar da hakkin mazauna yankin na Sudan mai fama da tashin hankali. Masanin al'amuran siyasa, na Sudan, Magdi El Gizouli yace hakan ya nunawa mazauna yankin na Darfur cewar:

"Da farko abin da hakan yake nufi a garesu shine, kowa na iya aikata mummunan laifin da ya ga dama ba tare da tsoron za a hukunta shi ba. Kasashen duniya kuma, sakamakon karancin ikon da suke dashi na siyasa, babu wani mataki da za su iya dauka, ko da suna son yin hakan".

Ranar Jumma'ar da ta wuce, babbar mai gabatar da masu laifi gaban kotun ta kasa da kasa ta birnin The Hague, Fatou Bensouda ta shaidawa kwamitin sulhun majalisar dinkin duniya cewar ofishin ta ya dakatar da binciken shugaban Sudan Omar Hassan Al-Bashir, bisa zargin laifin kisan kare dangi. A shekara ta 2009 ne kotun ta gabatar da takardun neman a kamo mata Al Bashir da wasu yan Sudan biyar. To amma babu wani mataki da majalisar dinkin duniya ta dauka a bangarenta domin ganin an kama wadanda ake tuhumar. A daura da haka ma, an rika yiwa binciken kotun cikas, ba tare da majalisar dinkin duniya ta tsawatar ba, saboda haka tace babu abin da ya rage mata, illa ta dakatar da binciken kan yankin Darfur.

Sudan Angriff auf Flüchtlingslager in Khor Abeche 06.04.2014
Yankin Darfur da yaki ya lalataHoto: Reuters

Nasara kan kotun yan mulkin mallaka

Masana sun yi hangen cewar babu yiwuwar nan gaba za'a sake neman kama Al Bashir saboda laifukan yakin na yankin Darfur. Kotun ta kasa da kasa ta dogara ne ga goyon bayan gwamnatocin kasashe, game da aiwatar da kiranta na kama wadanda ake tuhuma. Hanya daya ta tabbatara da haka kuwa, ita ce ta matsawa gwamnatocin lamba, tare da kudirin kamitin sulhu. To sai dai masanin siyasa, El Gizouli yace baya zaton hakan zai samu.

"Babu wani abu da zai nuna cewar kwamkitin sulhun, wanda ma a da can bai dauki wani mataki ba, nan gaba zai amince da matsawa gwamnatocin lamba. Ni kaina ba na zaton hakan zai faru. Ban tsammani kwamitin sulhun zai sami goyon baya na kasa da kasa domin ci gaba da farautar Omar Al Bashir ba. Wannan al'amari babu ma maganar a yanzu".

Wannan ma shine ra'ayin da masani a bangaren Afirka na kungiyar neman kare tsirarun kabilu reshen Jamus, Ulrich Delius ya nunar, wanda yace wannam mataki da Fatou Bensouda ta dauka wata alama ce, domin nunawa kwamitin sulhu cewar aiyukan kotun sun gagara, saboda kwamitin ya kasa tabuka wani abin kirki na goyon bayan wannan kotu. Shekara da shekaru suna lura da canjin ra'ayi da ake samu a manufofin kasashen Turai, musamman Jamus a game da kasar Sudan.

Fatou Bensouda
Fatou Bensouda ta kotun kasa da kasa a HagueHoto: Reuters

"Yace bisa manufa, wannan matakin da kotun ta kasa da kasa ta dauka a yanzu, yana nunawa al'ummar farar hula ne cewar ku sani fa, yanzu ba ku da wata kariya. Ku manta da abubuwan da suka faru a can baya. Yanzu kowa yana iya aikata manyan laifukan da yaso, saboda duk wanda ya aikata irin wadannan manyan laifuka ya san cewar babu wani da zai kaishi gaban kotu don ai masa hukunci".

A bayan kasar Sudan ma, wannan kudiri da kotun ta kasa da kasa ta birnin The Hague ta dauka yana da muhimaci. Kotun mai hukunta masu laifukan yaki da kisan kare dangi dama tana fama da muhawara tsakanin gwamnatoci da shugabannin kasashen Afirka, ganin cewar ya zuwa yanzu mafi yawan shari'ointa sun fi ne kan yan Afirka. Saboda haka ne ma shugaban Sudan Omar Hassan Al Bashir, yayi ikirari, bayan da kotun ta dakatar da bincike kansa cewar ya sami nasara kan kotun 'yan mulkin mallaka. 'Yan kwanaki kalilan ne kafin hakan, kotun ta dakatar da shari'ar da take yiwa shugaban Kenya, Uhuru Kenyatta, saboda karancin shaidu da za su baiyana gabanta.