Koriya ta Kudu ta shawarci Amirka da Koriya ta Arewa | Labarai | DW | 28.02.2019
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Koriya ta Kudu ta shawarci Amirka da Koriya ta Arewa

Shugaban kasar Koriya ta Kudu Moon Jae In ya baiyana takaicinsa game da yadda ganawar takwarorinsa na kasashen Amirka da Koriya ta Arewa ta kasance ba tare da cimma wata matsaya ba.

Watanni takwas da suka gabata ne shugaba Donald Trump na Amirka da shugaba Kim jung Un na Koriya ta Arewa suka gudanar da irin wannan taro a kasar Singapore sai gashi a karo na biyu ma basu cimma matsaya ba a batun lalata makaman Nukiliyar Koriya ta Arewa duk kuwa da cewar Shugaba Moon na Koriya ta Kudu na cigaba da taka rawa a batun a matsayinsa na hannun daman kasar ta Amirka, bayan ingantuwar dangantaka a yankin na Koriya Shugaba Moon ya gana da Kim sau uku a shekarar data gabata kan makan Nukiliya mallakar Koriya ta Arewa.

 

Sauti da bidiyo akan labarin