Koriya ta Kudu na inganta makaman yaki | Labarai | DW | 13.09.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Koriya ta Kudu na inganta makaman yaki

A wani mataki na tauna aya dan tsakuwa taji tsoro, Koriya ta Kudu ta ce ta cimma nasarar karawa dakarun sojojinta karfi dai dai da zamani ta hanyar sarrafa makami mai cin nisan zango.

Ma'aikatar tsaron kasar Koriya ta Kudu ne ta bayyana wannan mataki inda ta ce makamin da aka kerashi a kasar Jamus, zai cimma nisan zango da ya kai Kilomita 500 kuma an kera makamin da wasu sinadarai da zai kareshi daga dukkanin abin da zai hanashi cimma wurin sauka a yankunan abokan hamayya.

Koriya ta Kudu dai ta nade kafar wando na lalubo sabbin dabarun inganta karfin sojojinta, a matsayin kare kai daga barazanar makaman kare dangi daga makociyar ta Koriya ta Arewa.