Koriya ta Arewa ta yi sabbin gwaje gwajen makaman nukiliya. | Labarai | DW | 12.02.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Koriya ta Arewa ta yi sabbin gwaje gwajen makaman nukiliya.

Ƙasashen duniya na ci- gaba da mayar da martani da kakkausar ga Koriya ta Arewa,dangane da abin da suka kira karya dokokin ƙasa da ƙasa.

Babban sakataran Majalisar Ɗinkin Duniya Ban Ki Moon a cikin wata sanarwa da kakakinsa ya baiyana, ya ce wannan gwaje gwaje sun saɓama dokokin kwamitin sulhu na MDD.Shugaba Barack Obama na Amirka ya sanar da cewar yunƙurin tsokana ce, kana kuma barazana ga Amirka da kuma yankin baki ɗaya.

Ministan harkokin waje na ƙasar Rasha Sergei Lavrov ya ce sun gargaɗi Koriya da ta yi watsi da shirinta tare da mutunta dokokin MDD.Yayin da ƙasar China ta yi kira ga ƙawarta da ta bi ummarnin dokokin ƙasa da ƙasa tare da gayatar jakadin Koriya ta Arewa domin ba da baiyani.Nan gaba kuma a ka shirya kwamitin sulhu na MDD zai yi wani zama na musammun domin ɗaukar matakan ladabtarwa a kan Koriya ta Arewa, wacce tuni ta sanar da cewar baza ta fasa yin gwaje gwajen ba.

Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Mohammed Awal Balarabe