Koriya ta Arewa ta yi gwajin rokoki | Labarai | DW | 14.08.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Koriya ta Arewa ta yi gwajin rokoki

Hukumomin tsaron kasar Koriya ta Arewa sun tabbatar da harba wasu rokoki guda uku masu gajeran zango a yankin gabashi na gabar tekun kasar.

Hakan na zuwa ne 'yan lokuta kalilan kafin isar Fafaroma Francis a birnin Séoul na kasar Koriya ta Kudu, inda yake gudanar da wata ziyara ta kwanaki biyar.

An harba rokokin ne daga birnin Wonsan da ke da tashar ruwa a Koriya ta Arewa, inda rokokin suka ci zango na kilomita 220 kafin su fadi cikin yankin ruwan na Koriya. Roka ta karshe an harba ta ne mintuna 35 kafin lokacin isowar Fafaroma a wani barakin sojan saman birnin Seoul inda zai fara ziyarar.

A ranar Litinin mai zuwa ce dai, kasar Amirka da Koriya ta Kudu, za su fara wani attisaye na hadin gwiwa, wanda Amirka ta ce attisaye ne na kariya, yayin da Koriya ta Arewa ke ganin wani mataki ne na shirin yaki.

Mawallafi: Salissou Boukari
Edita : Mohammad Nasiru Awal