Koriya ta Arewa ta yi gwajin makamin nukiliya | Labarai | DW | 06.01.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Koriya ta Arewa ta yi gwajin makamin nukiliya

A wani mataki na kara nuna karfin da take da shi a fagen makammai a duniya, kasar Koriya ta Arewa ta sanar da yin wani sabon gwajin bam na hydogene mai karfin igiyar ruwa.

Kim Jong Un

Kim Jong Un

Kasar Koriya ta Arewa, ta sanar yin gwajin nata ne a wannan Laraba, wanda ake ganin idan har hakan ta tabbata, to wani babban cigaba ne da kasar ta yi wajan tsarinta na nukiliya. Sai dai tuni fadar shugaban kasar Amirka ta mayar da martani kan wannan batu, inda ta ce idan har hakan ta kasance gaskiya, to abu ne da ya sabawa yarjejeniyar kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya.

Daga nashi bangare Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya kira wani taron gaggawa a wannan Laraba domin tattaunan wannan batu na sabon gwajin nukiliyar kasar ta Koriya ta Arewa, inda wani jami'in diflomasiyya da bai so a bayyana sunan sa ba, ya ce taron zai gudana da yammaci kuma zai kasance na sirri.