Koriya ta Arewa ta yi faretin nuna kwanji | Labarai | DW | 08.02.2018
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Koriya ta Arewa ta yi faretin nuna kwanji

Kasar Koriya ta Arewa ta yi faretin soji na tauna tsakuwa domin aya ta ji tsoro gabanin gasar wasannin Olympics na lokacin sanyi hunturu.

Koriya ta Arewa ta gudanar da gagarumin faretin soji sa'oi 24 gabanin bude gasar wasannin Olympics na lokacin sanyin hunturu.

Kasaitaccen bikin ya hada da zagayowar cika shekaru 70 da kafuwar kasar Koriya ta Arewa.

Shugaban Koriya ta Arewa Kim Jong Un ya karbi gaisuwar ban girma na faretin dubban sojoji. 

Wasu yan Koriya ta Kudu sun baiyna cewa wannan matakin farko ne na yiwuwar sake hadewar yankunan biyu na Koriya a nan gaba.