Koriya ta Arewa ta sake harba sabon makami | Labarai | DW | 04.07.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Koriya ta Arewa ta sake harba sabon makami

Koriya ta arewa ta sake harba wani makami mai linzami a lokacin da Amirka ke shirin bikin 'yancin kai. Makamin da ya yi tafiyar likomita 930, ta harba ne yayin da hankalin Amirka ke ci gaba da tashi kan gwaje-gwajen.

Lamarin dai ya kai ga cikin gaggawa, shugaban Amirka Donald Trump wallafa sakon martanin nuna fushi a shafinsa na Twitter. Shugaba Trump a sakon nasa, ya yi kiran kasar China musamman ta kawo karshen barazanar Koriya ta arewar kowa ya huta.

Masu sharhi dai na cewa makamin da Koriya ta arewar ta harba, na iya rusa birnin Alaskan Amirka, daga wajen da aka harbo shi ba tare da samun wani tsaiko ba. An dai harbo makamin ne wanda ya yi tafiyar kilomita 930, daga arewacin lardin Phyongan, a dai dai lokacin da hankalin Amirka ke ci gaba da tashi kan gwaje-gwajen makamian kasar Koriya ta arewan.