1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Koriya ta Arewa ta kare kanta a MDD

Gazali Abdou Tasawa
August 29, 2017

Koriya ta Arewa ta bayyana harbin makami mai lizzami da ta yi a wannan Talata a matsayin wani martani ga atisayen sojojin na hadin gwiwa da Amirka ke yi da Koriya ta Kudu a yankin. 

https://p.dw.com/p/2j207
Nordkorea Kim Jong-Un
Hoto: Getty Images/AFP/STR

Koriya ta Arewa ta bayyana harbin makami mai lizzami da ta yi a wannan Talata a matsayin wani martani ga abin da ta kira mugun nufin  Amirka  da ke ci gaba da gudanar da atisayen sojojin na hadin gwiwa da Koriya ta Kudu a yankin . 

Jakadan Koriya ta Arewa a Majalisar Dinkin Duniya Han Tae-Song ya bayyana haka a lokacin wani taron da Majalisa Dinkin Duniyar ke gudanarwa kan batun makamai a birnin Geneva: 

"Koriya ta Arewa za ta ci gaba da karfafa matakan tsaronta da suka hada da makamin nukiliya matsawar Amirka  ba ta fasa yi ma ta barazana da ci gaba yin atisayen sojoji kusa da ita ba"