Koriya ta Arewa ta harba wani makami mai linzami | Labarai | DW | 28.07.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Koriya ta Arewa ta harba wani makami mai linzami

Koriya ta Arewa ta sake harba wani makami mai linzami, makonni uku da harba wani mai cin tazarar da ke iya isa wani sashe na Amirka.

Rundunar sojin kasar Amirka ce dai ta sanar da sabon gwajin makamin na Koriya ta Arewa, sai dai bata yi karin haske ba, tana mai cewa tana kan bincika lamarin.

Su ma dakarun kasar Koriya ta Kudu da Firaminista Shinzo Abe na kasar Japan, sun tabbatar da gwajin na yau, kasashen da tuni suka kama taron manyan hafsoshin tsaro.

Tun bara ne dai yawan gwaje-gwajen manyan makaman ke dagula fahimtar juna tsakanin kasar da wasu kasashen, musamman ma Amirka. A 'yan kwanakin da suka gabata ne dai Amirka da Koriya ta Kudu suka yi gargadi kan take-taken Koriya ta arewar.