korea ta Arewa tana shirin rufe cibiyar shirinta na makamashin nukiliya,abisa yarjejeniya da suka cimma aBeijing | Labarai | DW | 13.02.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

korea ta Arewa tana shirin rufe cibiyar shirinta na makamashin nukiliya,abisa yarjejeniya da suka cimma aBeijing

Kasar korea ta Arewa zata rufe wurin gudanar da shirin ta na mukamashin nukiliya da ke Yongbyon,domin baiwa masu bincike tsakanin kasa da kasa damar shiga,a bisa matakin farko na yarjejeniyar da aka cimma a birnin Beijing na kasr Sin.

A bisa wannan yarjejeniya da aka cimma dai, kasar korea ta Arewar zata yi hakan ne cikin kwanaki 60,wanda daga bisani ta sami mai na ton dubu hamsn(50),ko kuma agaji a fanin tattalin arziki dai dai darajar.

Kasashen 6 dai sun cimma wannan yarjejeniyar ce bayan ganawa da aka fara tun ranar alhamis da ta shige.