Korar Metin Kaplan daga Jamus | Siyasa | DW | 13.10.2004
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Korar Metin Kaplan daga Jamus

A jiya talata mahukuntan Jamus suka danka wa jami'an tsaron kasar Turkiyya Metin Kaplan da ake zargi da makarkashiyar kisan gilla a nan Jamus da kuma neman ta da zaune tsaye a Turkiyya

An dai dade ana famar kai ruwa rana a game da korar Metin Kaplan, mai kiran kansa Khalifan Kolon, daga nan Jamus domin danka shi ga hannun mahukutan Turkiyya, inda ake zarginsa da shirya makarkashiyar wani harin da aka yi niyyar kaiwa kan makabartar uban kasar Turkiyya Kemal Atatürk, bisa manufar kisan dubban sojoji da sauran magabata masu martaba a wannan kasa a misalin shwekaru shida da suka wuce. Kaplan dai shi ne shugaban wata kungiyar dake fafutukar kirkiro wata daula ta Khalifa, wacce aka haramta ayyukanta a Jamus, an kuma taba yanke masa hukuncin daurin shekaru hudu da rabi a gidan kurkuku sakamakon kiran da yayi na yi wa wani abokin takararsa kisan gilla. Akwai Musulmi da dama a nan kasar dake marhabin da wannan matakin da mahukunta suka dauka. Kuma ko da yake galibi ba wanda ya fito fili da wannan bayani, amma fa binciken da aka gudanar na ra’ayin jama’a ya nuna cewar da yawa daga Jamusawa na daridari da addinin Musulunci. Yawa-yawanci da zarar an yi batu a game da Musulunci, farkon abin da zai zo zukatan Jamusawa shi ne matsalar gani-kashe-ni da danne hakkin mata da kuma ta’addanci. Gaba daya dai an bata sunan addinin Musuluncin dake dada samun karbuwa a sassa dabam-dabam na duniya. Ba kuwa kafofin yada labarai ne kadai ke da laifin wannan ci gaba ba, kazalika har da wasu ‚yan tsiraru masu zazzafan ra’ayi irinsu Metin Kaplan, wadanda ke mummunan tasiri a zukanatan jama’a sakamakon fafutukarsu ta ikirarin yada addini, amma a zahiri wata manufa ce ta siyasa suke kokarin cimmawa. Ita kungiyar ta daular Khalifa, ba shakka tana tattare da barazana kuma a sakamakon haka aka haramta ayyukanta, amma a hakikanin gaskiya ana iya kwatanta kungiyar tamkar wata darika ta addini, wacce bata da wani kakkarfan goyan baya. Ba kuwa Jamusawa kadai ba hatta su kansu Turkawa da sauran Musulmi dake nan kasar suna Allah Waddai da manufofin Metin Kaplan, mai kiran kansa wai Khalifan Kolon, yana mai bata sunan musulmi da zub da martabar Musulunci a idanun jama’a. Dangane da kasar Turkiyya kuwa danka mata Kaplan da aka yi wata babbar kalubala ce, saboda shari’arsa zata zama tamkar zakaran gwaji a game da sabuwar alkiblar da kasar ta dosa a kokarinta na neman shigowa inuwar Kungiyar Tarayyar Turai. Ita dai fadar mulki ta Ankara tana sane da cewar dukkan kasashen kungiyar zasu sa ido domin bin diddigin shari’ar tasa kuma ta la’akari da haka da wuya mahukuntan kasar su yi kurarin azabtar da shi a gidan kurkuku. Amma abin tambaya kuma shi ne ko Ya-Allah kotunan kasar ta Turkiyya zasu yi amfani ne da shaidar da suka tara ta hanyar azabtar da magoya bayan Kaplan da aka tsare tun misalin shekaru shida da suka wuce domin zama ginshikin wannan shari’a. Muddin ba tantance wannan matsalar aka yi ba to kuwa mai yiwuwa wannan shari’a ta ci gaba har sai Illa-Masha-Allahu.