1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kongo: 'Yan adawa sun yi kiran zanga-zanga

Abdullahi Tanko Bala
December 28, 2018

Gungun 'yan adawa a jamhuriyar Dimukradiyyar Kongo ta yi kiran zanga-zangar gama gari a gabashin kasar bayan hukumar zabe CENI ta sanar da jinkirta zaben a gundumomin biyu.

https://p.dw.com/p/3AiLG
DR Congo Beni
Hoto: DW/J. Kanyunyu

A gabashin lardin Kivu yankin da jinkirta zaben ya fi shafa, daruruwan jama'a sun yi dandazo a birnin Beni domin nuna bacin ransu. Yayin da a gundumar Goma masu zanga-zangar suka sanya shingaye akan hanyoyi tare da hana zirga zirgar ababen hawa.

Kawancen jam'iyyun adawa ta Lamuka dake goyon bayan dan takarar adawa Martin Fayulu ta bukaci yin zanga-zangar a birane domin tsayar da al'amura cik a yau juma'a kwanaki biyu gabanin ranar zabe.

A daya bangaren kuma wata takaddamar diflomasiyya ta barke tsakanin gwamnatin da kungiyar tarayyar Turai, inda mahukuntan Jamhuriyar Dimukradiyyar Kongon suka bukaci jakadan Kungiyar tarayyar Turai a Kinshasa ya tattara ya fice daga kasar cikin sa'oi 48, matakin da kungiyar tarayyar Turan ta ce ko kadan bai dace ba.

Zaben wanda aka dade ana jinkirta shi, zai kasance zaben shugaban kasa na farko a Jamhuriyar Dimukradiyyar Kongo a cikin shekaru bakwai.