1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Gobara ta lalata kayan zabe a Kinshasa

Gazali Abdou Tasawa
December 13, 2018

Wata gobara da ta tashi a dakin ajiyar kayan zabe na birnin Kinshasa a Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango, ta lalata kayan zabe da suka hada da na'urar zabe ta zamani wacce bangarorin siyasar kasar ke da sabani kanta. 

https://p.dw.com/p/3A2UX
Pakistan - Brand in Textilfabrik in Karachi
Hoto: picture-alliance/dpa/R. Kahn

 

Shugaban hukumar zabe mai zaman kanta ta kasar Corneille Nangaa wanda ya tabbatar wa da tashar DW da afukwar lamarin ya ce kayan zaben birnin Kinshasa ne gobarar ta lalata inda amma ya ce wannan ba zai kawo cikas ga ci gaban shirye-shiryen zabukan kasar ba.

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da ya rage kwanaki 10 a gudanar da zaben shugaban kasa inda yanzu haka ake ci gaba da yakin neman zabe wanda sannu a hankali ke rikidewa zuwa tashin hankali a wasu yankunan kasar inda ko a wannan Alhamis wani dan sanda ya bindige har lahira wani matashi dan shekaru 17 magoyin bayan dan takarar adawa Felix Tshisekedi a garin Mbuji-Mayi na tsakiyar kasar inda dan adawar ke shirin gudanar da taron gangamin siyasa a wannan rana.