Komitin sulhu ya kusa cimma yarjejeniya akan Iran | Labarai | DW | 29.03.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Komitin sulhu ya kusa cimma yarjejeniya akan Iran

Jamian diplomasiya na komitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya sun bada rahoton cewa,membobi 5 na komitin suna gab da cimma yarjejeniya akan yadda zaa bullowa shirin nukiliya na Iran.

Bayan mika jerin wasu sabbin shawarwari,akwai alamun cewa,kasashen Burtaniya,Sin,Faransa,Rasha da Amurka nan bada jiamawa ba zasu sanya hannu kann yarjejeniyar,wadda zata bukaci Iran data dakatar da aiyukan inganta sinadaren uraniyum kamar yadda hukumar kula da kare yaduwar nukiliya ta bukace ta da tayi.

Komitin sulhun ya kwashe makonni 3 yana kokarin cimma yarjejeniya da zata gamshi dukkan membobi game da shirin na Iran,wanda kasashen Rasha da Sin suke nuna damuwa a kansa.

Wannan yarjejeniya ta zo kwana daya kafin taron ministocin kasashan komitin sulhun da kuma Jamus a Berlin domin tattauna batun nukiliya na kasar Iran.