Komitin Sulhu na Majalisar Dinkin Dunia zai kara yawan sojojin shiga tsakani a Cote D´Ivoire | Labarai | DW | 07.02.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Komitin Sulhu na Majalisar Dinkin Dunia zai kara yawan sojojin shiga tsakani a Cote D´Ivoire

Komitin sulhu na majalisar Dinkin Dunia, ya rataba hannu a kan dokar kara yawan dakarun shiga tsakani a kasar Cote D`Ivoire.

A sakamon wannan kuduri majalisar z ata kara sojoji 200 da ke zaune a Liberia tare da motoci masu sulke 14, da wasu karin 18 na zirga zirga.

Saidai Amurika ta hau kujera naki a kan wani saban yunkurin da sakataran Majailsar Koffin Annan yayi, na kara tura yan sandar kasa kakasa da kasa kimanin a Cote D´Ivoire.

Amurika ta yi korafin cewa karin yawan yan sanda ba za shi taimaka ciwo kan wannan rikici ba, muddun bangarorin da abun ya shafa, basu yi katabur ba, ta hanyar bada hadinkai.

A halin yanzu, rundunar kwantar da tarzoma ta majalisar Dinkin Dunia a kasar Cote D´Ivoire, ta kunshi sojoji dubu 7, da yan sanda dari 7, tare da karin sojojin Faransa dubu 4.

Saidai yawan sojojin, bai hana yaduwar tashe tashen hankulla,ba inda a jiya mutane 12 su ka rasa rayuka a cikin wata arangama da ta wakana,a wani kauye da ke yammacin kasar.