Komawar Buhari gun Likita na haifar da zargin gazawa | Siyasa | DW | 08.05.2018
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Komawar Buhari gun Likita na haifar da zargin gazawa

Shugaba Muhammadu Buhari bai boye aniyarsa ta sake komawa birnin London don sake duba lafiyarsa ba, amma babbar jam'iyar adawa ta PDP na ganin alamun kasawa a cikin harkokin iya gudanar da mulkin.

Tun bayan bayyana sake komawar shugaba Buhari birnin Londan, babban birnin tarayyar Najeriyar Abuja dama sauran sassan kasar sun dau dumi kan ziyarar ganin yadda lamuran siyasar kasar ke ci gaba da daukar zafi na sabbin rigingimun siyasa. Shehu Musa Gabam shi ne sakataren jam'iyyar SDP ta adawa, kuma a fadarsa Najeriya bata bukatar yanayin lafiya da rashinta.

"Akwai matsalar rashin lafiya wanda shi shugaban kasa ya san da ita, wanda shi kansa ya san cewa sake neman mulki ba zai zama alheri ba ganin shekaru da rashin lafiya da ya ke fama. Ina fatan za su sake lissafi."

Nigeria Regierungspartei PDP

Jam'iyar PDP tace tana ganin damar Buhari a zabe mai zuwa

Sarka mai rikicin gangan ko kuma kokari na cika burin siyasa, in har akwai bukatar sauyin taku a banagren 'yan APC dai daga dukkan alamu rashin lafiyan shugaban ya fara razana zukatan 'yan PDP acewar Dr. Umar Ardo dake zama jigo a babbar jam'iyyar adawa ta PDP.

"Tabbas rashin kuzarin shugaban zai haddasa shakku a zukatan 'yan APC har ma da jam'iyyar PDP, saboda muna fata Buhari ya tsaya zabe saboda zai zama karamar danga mai saukin kayarwa a ranar zabe."

Gano lago na shugaban kasa ko kuma cika baki na siyasa dai, suma al'umma sun bi sahu ga karatun na Buhari a London, kuma a fadar Dr. Usman Abdullahi sai Buhari ko kafar katako a ko yaushe.

"Mutum ya duba lafiyar sa abune daban, ko tsohon shugaban Najeriya yana zuwa duba lafiyarsa a waje, amma ba a yi masa fatan mutuwa. Wannan ina ganin 'yan siyasa ne kawai ke amfani da zantuttuka don a kawar da hankalin mutane. Mu dai Allah ne ya kawo mana Buhari."

Afrika Nigeria - Präsident Muhammadu Buhari

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari

Ko bayan batun sake takara, Shugaban na shirin  zuwa neman likita ne a lokacin da ma'ikatan asibitoci a kasar ke yajin aiki, abun kuma da ya toshe damar samun dama ta lafiyar miliyoyin 'yan kasar. To sai dai kuma kakain fadar shugaban Malam Garba Shehu na ganin akwai rashin adalci masu tunani na siyasa da batun yajin aikin ma'aikatan jinya.

"Buhari ya samu sauki sosai tunda ya dau lokaci bai waiwayi likitocinsa ba, batun yajin aiki kuma akwai jami'an da hakki ya rataya a kansu wajen tattauna matsalolin yajin aikin ma'aikatan lafiya a Najeriya ba sai lallai da shugaba Buhari za su tattana ba." Abun jira a gani dai na zaman tasiri ta ziyarar ga siyasa da makomar al'umma ta kasar dake kara kusantar zabe a cikin yanayin rikici.