Koma baya ga shari′ar kisan kare dangi a Ruwanda | Afirka a Jaridun Jamus | DW | 08.02.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Afirka a Jaridun Jamus

Koma baya ga shari'ar kisan kare dangi a Ruwanda

A wani mataki na ba zata, kotun Majalisar Dinkin Duniya a birnin Arusha na kasar Tanzaniya, ta soke hukuncin da aka yanke wa tsoffin ministoci biyu na Ruwanda.

Bari mu fara da jaridar Neue Zürcher Zeitung wadda a labarinta mai taken hukuncin ba zata a Arusha, ta yi mamaki da hukuncin da kotun Majalisar Dinkin Duniya dake shari'ar ta'asar da aka aikata a Ruwanda ta yanke inda ta wanke wasu tsaffin ministocin gwamnatin Ruwanda daga laifin aikata kisan kare dangi.

"Kotun dake zama a birnin Arushan Tanzaniya ta saki mutanen biyu tsaffin ministocin gwamnatin kabilar hutun Ruwanda saboda rashin isassun shaidun da suka tabbatar da tuhumar cewa sun shirya kisan kare dangi a kan 'yan kabilar Tutsi a shekarar 1994. Wannan hukuncin ya zo ne shekara daya da rabi bayan wani sashe na kotun ya yanke wa mutanen biyu hukuncin daurin shekaru 30 a kurkuku bayan an same su da laifin ingiza mutane su aikata kisan kare dangi, amma a wannan mako kotun ta duniya ta soke wannan hukunci. Wannan sabon hukuncin dai a cewar jaridar, wani koma baya ne ga shari'ar gaba ki daya."

Rashin tabbas a Afirka ta Tsakiya

Ita kuwa jaridar die Tageszeitung ta mayar da hankali ne a kan kasar jamhuriyar Afirka ta Tsakiya tana mai cewa:

„‘Yan tawayen da a cikin watan Disamba suka kwace wani yanki mai girma na kasar sun shiga cikin gwamnati, amma sun zargi shugaban kasa da karya alkawari. A ranar 11 ga watan Janeru aka kammala babban taron samar da zaman lafiya a kasar Gabon, tare da bikin sanya hannu kan jerin yarjeniyoyi da suka hada da ta kafa gwamnatin rikon kwarya karkashin jagorancin 'yan adawa. Wannan gwamnati ce za ta shirya zaben gaba da wa'adi a shekarar 2014. Sai dai tun bayan wata sanarwar da aka watsa ta gidan rediyon gwamnati a ranar Lahadi game da wata dokar kafa gwamnati, ake yi ta ganin alamun sake komawa fagen daga. An jiyo Janar Mohamed Dhafane na kawancen kungiyar ‚yan tawayen Seleka na cewa ba za su shiga cikin wannan gwamnati ba, jim kadan bayan an ba shi mukamin ministan albarkatun ruwa, gandun daji da kuma muhalli. Sai dai an yi wa ‚yan tawayen adalci domin kamar yadda aka amince a cikin yarjejeniyar kasar Gabon, an ba su mukamin ministan tsaro wanda a lokaci guda shi ne kuma firaminista wanda aka ba wa jagoran Seleka Michel Djotodjia.“

Matsalar yunwa a Afirka ta Kudu

Yunwa a kasar Afirka ta Kudu inji jaridar Neues Deutschland inda ta rawaito gwamnati na nuni da wani rikici sakamakon hauhawar farashin kaya na kimanin kashi tara cikin 100 a shekara.

„Fiye da mutane miliyan 12 a Afirka ta Kudu na fama da barazanar yunwa, musamman a watan Janeru lokacin da ake fama da rashin aiki, ga kuma karancin abinci saboda yanayin sanyin hunturu a cikin kasar, da hauhawar farashin kaya, saboda haka da yawa daga cikin ‚yan kasar na kwana da yunwa. Kasar dai na ware kashi 20 cikin 100 na kasafin kudinta don samar da kayan abinci. A sauran kasashen Afirka da akasarin al'ummominsu ke zaune a yankunan karkara kuma ke rayuwa a kan aikin noma wannan adadin ya kai kashi 50 cikin 100. Mafi yawan talakawa a Afirka ta Kudu na kashe kusan rabin albashinsu don sayen abin sakawa bakin salati. Don ganin an samu mafita, gwamnati tare da hadin kan kungiyoyi masu zaman kansu ta kaddamar da shirin yaki da yunwa ta hanyar samar da lambuna a tsakiyar musamman a gidajen mutane, ko tsakanin kungiyoyi ko kuma makarantu.”

Mawallafi: Mohammad Nasiru Awal
Edita: Usman Shehu Usman