Koma baya a kokarin warware rikicin Boko Haram | Siyasa | DW | 23.10.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Koma baya a kokarin warware rikicin Boko Haram

Al'ummar da ke zaune a yankunan da ke fama da hare haren da a ke dangantawa da Kungiyar Boko Haram na ci gaba da zaman dar dar.

Duk da cewar rundunar sojin Najeriya ta bayyana kokarrin dakile ayyukan da a ke dangantawa da kungiyar nan da aka fi sani da suna Boko Haramun, kuma duk da dimbin dakarun da ta ware domin tinkarar matsalar, har yanzu hare hare na ci gaba da janyo mutuwar mutane da dama ciki kuwa harda su kansu jami'an tsaron, abin da yasa wasu ke cewar yaki da 'yan ta'addan da rundunar sojin ke cewar ta kulla na da wahalar gaske. Nnamdi Obasi, mai nazarin lamuran da suka shafi Najeriya ga kungiyar International Crisis Group da ke fafutukar warware rigingimu a duniya, ya ce da fa sauran aiki a irin hubbasar da jami'an tsaron ke cewar suna yi:

"A gaskiya ba a kai ga yin nasara a kan 'yan kungiyar Boko Haramun ba. Watakila an yi nasarar kawar da su daga yankunan da suke da karfi, amma a zahiri ba a yi nasara akansu ba, kuma ba a sauya tsattsauran ra'ayinsu ba, kuma har yanzu akidun da suka runguma na ci gaba da wanzuwa."

Titel: DW_KAS_Behrendt: Schlagworte: Nigeria, Konrad-Adenauer-Stiftung, Hildegard Behrendt-Kigozi Wer hat das Bild gemacht/Fotograf?: Katrin Gänsler Wann wurde das Bild gemacht?: 22. Oktober 2013 Wo wurde das Bild aufgenommen?: Abuja, Nigeria DW_ICG: Nnamdi Obasi, Nigeria-Analyst der nicht-staatlichen Organisation International Crisis Group

Hildegard Behrendt-Kigozi, shugabar gidauniyar Konrad-Adenauer, a Abuja

Tushen rikicin arewacin Najeriya

Rigingimun da ke da nasaba da kungiyar ta Boko Haramun dai ya fi samun gindin zama ne a yankin arewacin kasar, wanda yasa wasu masu nazari irinsu, Hildegard Behrendt, shugabar gidauniyar Konrad Adenauer da ke Abujan Najeriya bayyana cewar, matsalar ba ta rasa nasaba da rashin kyakkyawan shugabanci:

Ta ce "A tunanina kamar sha'awar ta gushe ne, domin da farko mutane sun za ta za su samu ingantacciyar rayuwar da a ka yi alkawarin samar musu. Tamkar dai 'yan siyasa da 'yan boko sun basu kunya ne. Ba abin da suka yi musu, kuma ma a tunanin al'umma ya kamata da ace wadanda ke wakiltar kungiyoyin da ke kishin addini, sun dauki alhakin mutunta dokokin da suka shafi addini a lokacin da suke rike da mukamai."

Ko da shike hukumomi a Najeriya sun kafa dokar ta baci a wasu jihohin da a ke ganin rikicin na Boko Haramun ya fi tsananta irin su Borno da Yobe, amma har a baya bayannan, akwai wasu hare haren da suka janyo mutuwar mutane da dama a jihohin biyu.

Titel: DW_Gen-Attahiru Schlagworte: Nigeria, Boko Haram, nigerianische Armee, General Ibrahim Attahiru, Sprecher der nigerianischen Armee Wer hat das Bild gemacht/Fotograf?: Katrin Gänsler Wann wurde das Bild gemacht?: 22. Oktober 2013 Wo wurde das Bild aufgenommen?: Abuja, Nigeria DW_Gen-Attahiru: General Ibrahim Attahiru, Sprecher der nigerianischen Armee, will die militärische Zusammenarbeit mit den Nachbarländern verstärken

Janar Ibrahim Attahiru

Hanyar warware kalubalen tsaro a Najeriya

Duk da ikirarin galabar da sojojin ke cewar suna samu a kan 'yan kungiyar, amma sun yi na'am da cewar, abin da ke kawo musu cikas shi ne tinkarar mutanen da ke yin yakin sunkuru. Wani lokacin ma a cewar kakakin rundunar sojin Najeriya, janar Attahiru Ibrahim, sukan tsallaka zuwa kasashen da ke makwabtaka da Najeriya:

"A fagen diflomasiyya ma muna tuntubar kasashen da ke da iyakoki da Najeriya ta yankin arewa maso gabas, kamar Nijar da Kamaru. Sai dai kuma 'yancin neman cimmusu kayyadadde ne, domin da zaran ka isa kan iyaka da wasu kasashe, ba za ka iya tsallaka wa domin gudanar da ayyukan soji ba. Abu mafi dacewar da zamu iya yi, shi ne hadin kai a tsakanin rundunoninmu."

Sun kansu jami'an tsaron Najeriya dai na shan suka daga kungiyoyin kare hakkin jama'a a ciki da wajen kasar bisa muzgunawar da suke yi wa jama'a da kuma wadanda suke zargi da kasancewa mambobin kungiyar ta Boko Haramun ne.

Masu sharhi dai sun bayyana bukatar daukar matakan warware matsalolin zamantakewa da ta tattalin arziki da kuma na siyasa, domin shawo kan rigingimun, maimakon mayar da hankali a kan matakan soji kadai.

Mawallafi : Gänsler, Katrin / Saleh Umar Saleh
Edita : Umaru Aliyu

Sauti da bidiyo akan labarin