Kokarin yaki da tsauraran akidu a yankunan Sahara da Sahel | BATUTUWA | DW | 01.06.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

BATUTUWA

Kokarin yaki da tsauraran akidu a yankunan Sahara da Sahel

A birnin N'Djamena na kasar Tchadi, ana gudanar da taron yaki da yaduwar akidar tsautsauran ra'ayin addini a kasashen Sahel da Sahara karo na biyu.

Makasudin taron dai shi ne nazarin hanyoyin tallafa wa jama'a musamman matasa ta yadda za a hana masu fadawa tarkon kungiyoyin masu tsatsauran ra'ayin adinin  da suka yadu a cikin yankin na Sahel da Sahara. Gazali Abdou Tasawa ya duba mana wannan batu, ga kuma rahoton da ya hada mana.

Yaduwar ayyukan ta'addanci mai nasaba da kaifin kishin addini da ake fuskanta a kasashen yankin Sahel da Sahara, wata matsala ce da ke ci gaba da ci wa al'umomin yankin dama na sauran sassan duniya tuwo a kwarya. Wannan ce ta sanya kasashen yankin tare da hadin gwiwar Majalisar Dinkin Duniya suka shirya wannan taro wanda ya hada duk wasu masu ruwa da tsaki a harkokin addini da tsaro na yankin. Lokacin taron za a yi musayar bayanai tare da fito da shawarwari dangane da hanyoyin da suka dace a bi wajen daukar matakan rigakafi na zahiri da za su taimaka don ganin an yi watsi da akidar tsautsauran ra'ayin addinin wacce ke matukar yin illa a yankin na Sahel da Sahara da kungiyoyin 'yan ta'adda da dama suka yi kaka gida a cikinsa.

Global Media Forum 2012 Die Redner Referenten Dr. Mohamed Ibn Chambas

Da yake tsokaci ga manema labarai a wajen taron manzo na musamman na Majalisar Dinkin Duniya a Afirka ta Yamma da Sahel, Mohamed Ibn Chambas, ya ce sai an dauki matakan bai daya, muddin ana son kawar da wannan matsalar daga yankin na Sahel.

Ya ce ''a soma da yin nazarin kan abubuwan da suka haifar da matsalar tun daga tushe, kamar matsalar jahilci da ta nuna wariya ga wasu rukunan al'uma da raunin da gwamnatoci wajen tafiyar da mulki a kasashe da dama na yankin Sahel da Sahara. Kenan sai tunkari matsalar ta hanyoyi daban-daban kamar na siyasa da tattalin arziki zamantakewa da kuma tarbiya"

Himmar Kungiyar tarayyar Afirka ga yaki da tsaurin ra'ayi

Batun kasar Mali da kungiyoyin 'yan ta'adda ke ci gaba da kafa doka da oda a yankunan tsakiya da ma arewacin kasar na daga cikin muhimman batuuwan da taron na birnin N'Djamena ya tattauna a kai. Kuma da yake tsokaci, wakilin kungiyar Tarayyar Afirka a Mali da Sahel, Manjo Pierre Buyoya, cewa ya yi yankin na Sahel ya zamo yankin da matsalar tsaro ta fi kamari a nahiyar Afirka. Ya kuma bayyana kokarin da Kungiyar Tarayyar Afirkar ke yi wajen ganin ta murkushe matsalar a wannan yanki.

"Ya ce Kungiyar Tarayyar Afirka ta dukufa wajen shawo kan matsalar yankin na Sahel musamman tun bayan barkewar rikici a kasar Libiya. Kuma kungiyar na gudanar da aikin nata ne a wannan yanki na Mali da Sahel bisa izinin MDD. Kazalika a nan kasar Tchadi ma kungiyar na a fagen daga. Ka ga kenan tana dagewa wajen ganin an samu zaman lafiya a baki dayan yankin na Sahel"

Wasu daga cikin muhimman batutuwan da taron na birnin N'Djamena ya tattauna dai sun hada da rawar da matasa da mata za su iya takawa wajen yin rigakafin yaduwar akidar tsattsauran ra'ayin a yankin na Sahel inda har kawo yanzu matakan da aka fi dauka wajen yaki da ayyukan ta'addanci sun fi mayar da hankali ne kan yin amfani da karfin soja maimakon duba hanyoyin inganta rayuwar al'uma da halin zamantakewar al'uma.

Sauti da bidiyo akan labarin