Kokarin tsagaita wuta a Syria | Labarai | DW | 23.07.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kokarin tsagaita wuta a Syria

Gwamnatin kasar Syria ta sanar da wata yarjejeniyar tsagaita buda wuta tsakanin mayakan tawaye da dakarun gwamnati, a fafatawar da ake yi a gabashin Ghouta da ke kusa da birnin Damascus.

An cimma matsayin ne bayan zaman neman sulhu da bangarorin biyu suka yi a birnin Alkahiran Masar, kamar yadda kasar Rasha mai dakaru a Syriar ta fada. Sai dai babu wata kungiyar tawaye da ta ce ta sanya hannu kan wannan yarjejeniya, musamman ganin yadda wata kungiya daga cikinsu ke nesanta kanta daga maganar.

Wannan labarin na zuwa ne bayan wani zama da aka yi a Syria a ranar 9 ga wannan watan na Yuli, kuma kasashen Amirka da Rasha da Jordan, su ne suka tsara dabarar tsagaita buda wa juna wutan a Syria.