Kokarin tabbatar da kariya da kuma ci-gaban mata | Siyasa | DW | 10.01.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Kokarin tabbatar da kariya da kuma ci-gaban mata

Duk da cewar samu karin ci-gaba ga shigar mata a matakai na mulki a Najeriya, akwai dai korafi na ci-gaban danniyar al'adu da ma manufofi game da makomar mata a cikin kasar.

A wani abun da ke zaman sabon yunkurin ta na tabbatar da amincewa da daukacin shirin tabbatar da muradin karni da ci-gaban mata a cikin tarrayar Najeriya, mataimakiyar sakataren Majalisar Dinkin Duniya mai kula da harkokin mata Michele Bachelet ta fara wata ziyarar aikin da za ta bata damar ganawa da daukacin masu ruwa da tsaki da harkokin kasar.

Duk da cewar dai an kai ga samun karin ci-gaba ga shigar mata a matakai daban daban na mulkin tarrayar Najeriya, akwai dai korafe korafe na ci-gaban danniyar al'adu da ma manufofi a bangaren mahukunta game da makomar mata da basu damar ci-gaba a cikin kasar.

Tabbatar da hakki da ci-gaban mata

Abun kuma da ya haifar da ziyarar dake zaman irin ta ta farko da kuma a cikin ta jami'ar ta ce ta je Abuja ne domin neman tabbatar da hakki da ci-gaban mata a matakai daban daban na kasar.

Nigeria Gewalt gegen Frauen in Afrika

Cin zarafin mata na bazaranar zama ruwan dare a wasu sassan Najeriya

Kama daga dokoki ya zuwa manufofin da suka shafi harkokin mata a matakai daban daban na kasar dai a cewar jami'ar da ta gana da shugaba Goodluck Jonathan a ranar Alhamis, Majalisar ta Dinkin Duniya ke kokarin ganin tabbatar da su a kasar da a cewar ta ke samun gagarumin ci-gaba.

"Mun yi magana kuma mun jaddada aniyar Majalisar Dinklin Duniya da ma ofishin kula da mata nata na ci-gaba da taimaka wa kokarin da tarrayar Najeriya ke yi ta fanni daban daban karkashin ministar harkokin mata domin inganta rayuwar matan da samar da lafiya da ilimi da kuma cimma muradun karni da ma duk abubuwan da mata ke bukata domin basu damar taimaka wa tattalin arzikin kasarsu, girman da zai iya tunkarar batutuwa kamar na isasshen abinci da sauyi ga muhalli da dai sauransu."

Bildergalerie Muslimisches Opferfest Eid al Adha 2012

Yara manyan gobe

Ana dai zargin majalisun tarrayar kasar da kin amincewa da dokar hana nuna wariya ga mata sannan kuma da gwmantin da ke jan kafa wajen rattaba hannu da aiwatar da jerin yarjeniyoyi da tanaje tanajen kasa da kasa kan hakokin matan.

Wasu al'adu na taka rawa wajen tauyen hakkin mata

Ko bayan nan kuma tsarin al'adun kasar da a wasu wuraren ya samar da banbanci ga batu na gado da kaciya ga mata da dai sauran banbancin al'adu dake zaman abun damuwa ga bakuwar da ma ragowar abokan takunta a majalisar abun kuma da a cewar Hajiya Zainab Maina ministar harkokin matan kasar ya kama hanyar sauyawa sakamakon ziyarar.

Abun jira a gani dai na zaman tasirin sauyi ga kasar ta Najeriya dake gine kan tsari na maigida namiji mace kuma mai taimako a gareshi a koyaushe.

Mawallafi: Ubale Musa
Edita: Mohammad Nasiru Awal

Sauti da bidiyo akan labarin