1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamus

Amirka: Kokarin sasanta rikicin Habasha

Ramatu Garba Baba
March 15, 2023

Antony Blinken ya isa kasar Habasha don gana wa da firaiminista Abiy Ahmed kan yiyuwar cimma yarjejeniyar zaman lafiya a tsakanin gwamnatin kasar da 'yan gwagwarmayar Tigray.

https://p.dw.com/p/4Oh9p
Sakataren Harkokin wajen Amirka Antony Blinken ya isa Ethiopia
Sakataren Harkokin wajen Amirka Antony Blinken ya isa EthiopiaHoto: Tiksa Negeri/AFP/Getty Images

A wannan Larabar, Sakataren Harkokin wajen Amirka Antony Blinken zai gana da firaministan Habasha Abiy Ahmed, a yayin wata ziyarar da ya kai kasar da zummar samar da mafita daga rikicin da ya daidaita kasar, har wa yau, jami’in zai yi amfani da wannan dama wajen cimma daidaito a huldar da ke tsakanin Amirka da Ethiopiya da ta yi tsami a sakamakon rikicin kasar da ake zargin Firaminista Abiy Ahmed da aikata ba daidai ba.

Blinken shi ne babban jami'in Amirka da ya ziyarci kasar da ta kasance ta biyu mafi yawan al’umma a Afirka baya ga Najeriya, tun bayan yakin da ya barke a karshen shekarar 2020 tsakanin rundunar gwamnatin Habasha da 'yan gwagwarmaya na yankin Tigray, matakin da firaiminista ya dauka a yakin ya janyo masa bakin jini da jerin takunkumai daga kasashen yamma musanman Amirka da yanzu ke kokarin dinke wannan barakar. Rikicin kasar ta Habasha ya lakume daruruwan rayuka baya ga wasu kusan miliyan guda da suka rasa matsuguni. Daga Habashan, Blinken zai kai ziyara a Jamhuriyar Nijar da ke fama da matsalolin tsaro a sakamakon ayyukan 'yan ta'adda.