1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kokarin sasanta rikicin Sudan ta kudu

December 27, 2013

Shugabannin kasashe makwabtan Sudan ta Kudu sun nuna goyon bayansu ga shugaba Salva Kiir a rikicin kabilancin da ya addabi wannan jaririyar kasa.

https://p.dw.com/p/1AhiW
Hoto: Reuters

A wani taro da suka yi a Nairobi babban birnin kasar Kenya, shugabannin sun ce ba za su yarda da wani mataki na hambarar da gwamnatin da aka zaba ta hanyar demokradiyya ba.

Shugabannin yankin gabacin Afirka a karkashin wata kungiya da ake kira IGAD sun fada a cikin wata sanarwa cewa sun yi maraba da kudurin gwamnatin Sudan ta Kudu na kawo karshen fadan nan-take. A karshen taron na birnin Nairobi, shugabannin yankin sun ce gwamnatin Sudan ta Kudun ta amince ta kawo karshen fadan, abin da ya sanya fatan samun wani ci gaba a kokarin dakatar da tashin hankalin da ya yi sanadiyar ta da mutane sama da dubu 120 a wannan jaririyar kasa a duniya.

A daina fada cikin kwanaki hudu

A lokacin da yake karanta sanarwar bayan taron Firaministan Habasha Hailemariam Desalegn ya ce idan ba a dakatar da fadan a cikin kwanaki hudu bayan wannan sanarwa ba, to taron kolin zai duba yiwuwar daukar wasu matakai.

Südsudan Juba Riek Machar Salva Kiir 09.07.2013
Riek Machar da Salva Kiir a bayaHoto: Reuters

"Za mu dauki matakan da suka dace na yin tattaunawa da kowa da kowa domin samar da kyakkyawan yanayi ta yadda dukkan masu ruwa da tsaki a rikicin za su gana ido da ido a ranar 31 ga watannan na Disamba."

Sai dai madugun 'yan tawaye kuma tsohon mataimakin shugaban kasa Riek Machar wanda dakarunsa ke fafatawa da na shugaba Salva Kiir bai halarci taron ba. Amma shugabannin sun yi kira gareshi da ya tsagaita bude wuta.

A wani jawabi a gun taron shugaban Kenya Uhuru Kenyatta ya ce akwai kafar tabbatar da zaman lafiya a Sudan ta Kudu. Taron na kungiyar ta IGAD ya nuna adawa da duk wani sauyin gwamnati da karfin tuwa a Sudan ta Kudu.

"Mu a IGAD ba za mu amince da kifar da wata gwamnati da aka zaba ta hanyar demokradiyya a Sudan ta Kudu ba. Tashin hankali bai taba kawo maslahar da ake bukata ba. Ba za mu yarda a ci gaba da kashe fararen hula ba. Muna tune da wahalhalun da al'umar Sudan ta Kudu suka sha a shekarun baya, dole ne a kawo karshen wannan tashin hankali."

Rikicin Sudan ta Kudu barazana ga yankin

Shugaban na Kenya ya kara da cewa idan ba a shawo kan wannan matsala ba, to za ta haddasa kwararar miliyoyin 'yan gudun hijira na cikin gida, wanda haka zai kawo mummunan koma baya ga yankin baki daya.

Südsudan Flüchtlinge Flüchtlingslager Juba
Tuni dai fadan ya haddasa kwararar 'yan gudun hijiraHoto: picture-alliance/dpa

"Duk wata maslaha ta soji a cikin gida ba za ta yi nasara ba. Wannan tashin hankalin zai haifar da wata fitina, da za ta yi wahala Sudan ta Kudu da ma yankin gaba daya su iya shawo kanta. Wata barazana ce a yankin da ba za mu amince da ita ba."

A ranar 15 ga watannan na Disamba rikici ya barke a Sudan ta Kudu sannan ya yadu kamar wutar daji. Manyan kasashen yamma da kuma gwamnatocin yankin na fargabar cewa rikicin kabilancin a Sudan ta Kudu ka iya rikidewa zuwa wani yakin basasa, abin da ka iya zama hadari ga yankin mai fama da rikici da kuma rashin cikakken tsaro a kan iyakokinsa.

Mawallafi: Mohammad Nasiru Awal
Edita: Usman Shehu Usman