1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya: Buhari ya gana da shugabannin addinai

March 29, 2019

Kasa da 'yan makonni da kammala zabukan tarrayar Najeriya mai zafi ne Shugaba Muhammadu Buhari ya gana da wasu shugabannin manyan addinan kasar biyu a wani abun da ake yi wa kallon kokari na sasanta tsakanin juna.

https://p.dw.com/p/3Fudm
Muhammadu Buhari
Hoto: DW/I. U. Jaalo

An dai kai ga tayar da jijiyar wuya cikin fagen siyasar tarrayar Najeriya sannan kuma kawunan sun kai ga rabewa a bisa turbar addini a  fagen siyasar. An ma kai ga zabukan kasar a cikin imanin rawa ta malaman addinin da suka fito fili da nufin nuna gwanayensu a zabukan kasar mai tasiri. To sai dai kuma ana shirin sake hade kai yanzu tare da wani taro na shugaban kasar da malaman addinanta biyu da nufin kau da banbancin dama fatan dorawa cikin ginin kasa.

Interfaith Mediation Centre in Kaduna
Fasto James Wuye tare da Imam Muhammad AshafaHoto: Katrin Gänsler

Najeriyar dai ta dauki lokaci tana fuskantar tsomin baki na masu siyasar da ake tallakawa da sakamakon da ke nuna shugaban kasar na tasiri a cikin sashen arewacin kasar a yayin kuma da aboki na hammayarsa ya taka rawar gani a bangaren kudu. To sai dai kuma daga dukkan alamu mahukunta na kasar na neman kaucewa rabuwar addinin tare da wata ganawa a tsakanin shugaban kasar da shugabannin manyan addinan kasar biyu.

Malaman addinin dai na dan jan aikin banbace zamowa fitila ta haska al'ummar da suke yi wa jagora da kuma fakewa a cikin sunan addinin da nufin tunzura magoya baya.