Kokarin kawar da kyama ga masu cutar AIDS ko SIDA | Siyasa | DW | 01.12.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Kokarin kawar da kyama ga masu cutar AIDS ko SIDA

Ranar daya ga watan Disamban kowacce shekara rana ce da aka ware don yaki da cutar AIDS ko SIDA. A irin wannan lokacin akan wayar da kan mutane game da illar cutar da kokari na kawar da wariyar da ake nunawa masu ita

A irin wannan rana, kasashen duniya kan gudanar da taruka domin fadakar da al'umma kan illolin wannan cuta da ma matakai da suka kamata a dauka wajen yakarta da nufin kawar da ita tsakanin al'umma. A jawabinsa albarkacin bikin na bana babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya Ban Ki-moon ya bukaci da a kawo karshen wariyar da ake nunawa masu dauke da cutar.

Gwamnatoci da kungiyoyin fararen hula da sauran kungiyoyi da ke bada agaji ta fannin kiwon lafiya sun gudanar da taruka da gangami duka dai da nufin ganin an hada hannu waje guda don samun nasarar kawar da cutar inda suka bayyana kirin matakan da suka dauka a hukumance don ganin hakarsu ta kai ga cimma ruwa.

HIV Aids Bekämpfung in Afrika UN Millenniumsziele

Masu dauke da cutar a wasu sassan Afirka na kokawa dangane da karancin magani

Tarayyar Najeriya ma dai ta bi sahun sauran kasashe wajen gudanar da biki inda a jihohi daban-daban da ke fadin kasar aka yi zama na musamman kan batun. Wakilinmu da ke Bauchi Ado Abdullahi Hazzad ya ce a Bauchi kungiyoyin masu dauke da cutar da kwamiti na musamman na yaki da cutar ta AIDS da jami'an gwamanti sun yi taro inda suka bukaci a kawar da kyama da ake nunawa masu dauke da cutar wadda a cewarsu itace babbar hanya ta kawar da yaduwarta.

To sai dai yayin da ake kokarin rage kaifin yaduwarta ko ma kawar da ita baki daya, wasu mutanen na korafin cewar rashin samun magunguna na rage kaifin cutar da ma karancin cibiyoyin kiwon lafiya da za su rika kula da masu dauke da ita na yin nakasu ga wannan yunkuri da ake yi. Sau tari dai gwamnatoci kan ce suna bakin koakrinsu wajen cike wannan gibi sai dai kungiyoyin masu dauke da cutar da sauran kungiyoyi na fararen hula na cewar wannan magana a fatar baki ta ke kawai.

Kowacce shekara akan yi addu'o'i na musamman da sanya furanni don tunawa da wanda cutar ta hallaka

Duk shekara ana yin addu'o'i da ajiye furanni don tunawa da wanda cutar ta hallaka

Wani bangare na taken bikin na bana dai shi hada karfi da karfe don samun al'umma da nan gaba za ta kasance ta yi hannun riga cutar AIDS ko SIDA to sai dai masu fashin baki ta fannin kiwon lafiya na ganin akwai jan aiki a gaba a yakin da ake da cutar ko da dai ana cike da fatan za iya kawar da ita baki daya daga nan zuwa shekara ta 2030 kamar yadda wata gamayya ta kungiyoyi da ke bada tallafi wajen yakar cutar ta shaida.

Hukumar Majalisar Dinkin Duniya da ke sanya idanu kan yaki da cutar ta AIDS ta ce cimma wannan buri na kungiyoyi na ganin bayan cutar zai ta'allaka ne da irin kokarin da aka yi wajen yakarta a shekaru biyar din da ke tafe.

Sauti da bidiyo akan labarin