1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kokarin kare Mozambik daga yaki

October 23, 2013

Gwamnatin kasar Mozambik da kungiyar Renamo sun bayyana shirin tabbatar da kare kasar daga sake fadawa cikin yakin basasa.

https://p.dw.com/p/1A5DS
Hoto: picture-alliance/dpa

Gwamnatin kasar Mozambik da kungiyar Renamo sun bayyana shirin tabbatar da kare kasar da sake fadawa cikin yakin basasa, bayan 'yan tawayen na Renamo sun fice daga cikin yarjejeniyar tsagaita wuta ta shekarar 1992.

Shugaban kasar ta Mozambik Armando Guebuza ya jaddada shirin tattaunawa, a matsayin mafita guda da a ke da ita. Sannan tsaffin 'yan tawaye da suka zama 'yan adawa sun ce babu bukatar sake jefa kasar cikin yakin basasa.

Harin da dakarun gwamnati suka kai sansanin 'yan tawaye, da kuma martanin da 'yan suka kai kan ofishin 'yan sanda a garin Maringue na yankin tsakiyar kasar, ya jefa tsoro kan sake fadawar kasar cikin rikici.

Rainer Tump ya san kasar ta Mozambik a shekaru masu yawa da suka gabata, sannan yana aiki a matsayin jami'in wata kungiya mai aikin raya kasa ta hadin gwiwa tsakanin kasar ta Mozambik da Jamus:

"Babban abin shi ne kungiyar Renamo tana neman kare kanta cikin shekarun da suka gabata, saboda rashin taka katabus a zabukan da suka gabata na kasa da na kananan hukumomi. Wannan shi ya sa shugaban kungiyar Afonso Dhlakama ya koma sasaninsa."

Kasar ta Mozambik tana cikin wadanda ke kan gaba wajen samun bunkasa tattalin arziki a duniya, haka ya samu ne, saboda yarjejeniyar tsagaita wuta ta shekarar 1992, wadda ta kawo karshen yakin basasa na tsawon shekaru 16, wanda ya yi awun gaba da rayuka mutane kimanin milyan guda.

Mosambik Krise Flüchtlinge
Hoto: picture-alliance/dpa

Carla Turrini ta chocin Katolika tana cikin wadanda suka taimaka a ka kulla yarjejeniyar zaman lafiya ta shekarar 1992 tsakanin 'yan tawayen Renamo da gwamnatin Frelimo:

"Ina tunanin cewa har yanzu akwai dama ta tattaunawa, domin kare sake fadawa cikin rikici. Ina tunanin cewa babu mai fatan ganin Mozambik ta sake shiga yakin basasa. Ina gani kowa ya yi farin ciki da shekaru fiye da 20 na zaman lafiya. Duk bangarorin za su iya zama domin yaki babu abin da zai haifar wa kasar."

An rufe makarantu cikin yankin da ake da sansanonin 'yan kungiyar Renamo. Tuni 'yan kasar suka fara bayyana begen da suke da shi, bisa daurewar zaman lafiya:

Unruhen in Mosambik
Hoto: picture-alliance/dpa

"Ina tunanin cewa akwai sauran dama ta tattaunawa, domin shawo kan matsalar."

"Ina ganin shugaban kasa zai yi abin da ya dace. Kuma idan wani bangare ya wuce gona da iri haka zai iya jefa kasar cikin yaki."

"Ina tunanin 'yan Mozambik sun fahimmaci mahimmancin zaman lafiya. Ina ganin za a yi duk abin da ya dace domin tabbatar da zaman lafiyar Mozambik."

Kasar Jamus tana cikin kasashen duniya da suka nuna damuwa kan abin da ke faruwa a kasar ta Mozambik. Martin Shäfer shi ke zama kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar:

"Jamus tana nuna damuwa tare da bin sahun abin da ke faruwa. Cikin shekarun da suuka gabata, Jamus ta ba da gagarumin taimakon raya kasa, wanda duk bangarorin kasar suka ci amfani kuma ya taimaka wajen samun zaman lafiya na siyasa. Kuma wannan hali da kasar ta shiga zai yi karar tsaye wa ci-gaba."

Shugaban kasar Armando Guebuza ya ce harin da dakarun gwamnati suka kai, sun yi domin kare kai, amma 'yan tawayen sun ce yunkuri ne na hallaka shugabansu.

Afonso Dhlakama shugaban tsahuwar kungiyar ta 'yan tawayen Renamo da ta zama jam'iyyar adawa, ya jagoranci daya daga cikin yakin basasa mafi dadewa a nahiyar Afirka. Kasashen duniya sun nemi kai zuciya nesa.

Mawallafi: Suleiman Babayo
Edita: Saleh Umar Saleh