Kokarin karbe iko da garin Ramadi | Labarai | DW | 26.05.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kokarin karbe iko da garin Ramadi

Mahukuntan Iraki sun ce sun matsa kaimi a yau na kai hare-hare kan 'yan kungiyar nan ta IS da suka karbe iko da garin nan na Ramadi a kwanakin da suka gabata.

Gidan talabijin din Irakin da ya tabbatar da wannan labarin ya ce sojin gwamnati ne gami da mayaka na kungiyoyin Sunni da na Shi'a ne suka shiga wannan aiki don maido da garin karshin ikon gwamnati.

Mai magana da yawun mayakan kungiyar Shi'a a Iraki din Ahmed al-Assadi ya shaidawa manema labarai cewar yunkurinsu na karbe iko da garin ba zai jima ba kuma yanzu haka sojin gwamnati sun yi wa garin kawanya.

Ya zuwa yanzu dai babu wani cikakken bayani game da cigaba ko akasin haka da aka samu a wannan fito na fito din da ake yi da IS a Ramadi din. Iraki dai na daga cikin wuraren da kungiyar IS ke rajin kafa daular Islama.